FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Preview
"Ina kud'in mai d'inkin suke? Allah Yasa baki mantasu can ba dai!" Wata mata ta furta a d'an k'age yayin da take shan wani layin tana tuka mota, tana baro layin Family house insu, dasu ka kaima ziyara."Wanne kud'in? Ni ba Wanda yabani wani kud'i" Yarinyar da Akalla bazata gaza shekaru 18 ba ta fad'a, kuma kallo d'aya zakamata kasan 'yar matar da ke driving d'in ce."Wani irin ba Wanda yabaki kud'i? Baby kud'in da nace ki dakk'o cikin wardrobe tun muna gida, zakicemini ba Wanda yabaki kud'i? Ba ke gimbiya tabasu ba ki ajiye tunda farko?" Matar ta furta a hasale, tana parking tsakiyar titin da take kai, dama hanyar ba wani wurin wucewar motoci baneba, irin hanyoyinnanne na cikin layi masu yashi."Mama Nikam bani gimbiya taba ajiyar kud'in ba, ba ita ta ajiye miki da kanta ba, inaji fah kamar kafin mu fito tana cemiki kud'in basu hannuna, ita ta ajiye" ta furta, idanunta na soma fidda kwalla,...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.