FreeArewaPen original
UWA ALJANNAR DUNIYA
- 1views
- 29chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · CHAPTER 1 EPISODE 1
GargadiBanyi wannan littafin dan cin zarafin wani ko wata ba. Nayi shi dan ya zama izna ga masu irin dabi'un. Jan kunne ne ga mazajen da ba su san darajar matayen aurensu ba. Haka kuma ishata ce, ga matayen da suke cin amanar gidajen aurensu,tare da bata duniyoyin 'ya'yansu musamman mata.Sadaukarwa.Na sadaukar ga wannan littafin, ga mijina. Bukhari Ibrahim Ladan. Ranka shi dade Allah ya ja kwana 👌🏻Shinfida✍🏻KatsinaLayin masanawaWani irin bak'in hadarine, yake ta rugugi a sararin samaniya. Misalin 'karfe biyar din yamma ne. Amma garin yayi wani irin duhu na damina. Ga sassanyar iska da take ta kad'awa. Ni'ima mai sanyi ta sauka a garin sosai.Wani madaidaicin gida na hango mai farin fenti. Hankalina ya koma kallon gidan da sha'awa. Kasancewar bishiyoyi ne ratata a cikin harabar gidan, sai rangaji suke. Ganyayyakin da suka bubbushe sunata kakkab'a.Gidane mai dauke da 'dakuna uku kacal. kallo 'daya zaka gane gidan na masu matsakaicin karfine. Ciki da falo na hango kabulen falon sai tashi sama yake. Sai d'aki daya daga gefe guda. Ga ban daki da d'akin girki, duk a tsakar gidan. Tsakar gidan madaidaicine, Wanda aka k'awata shi da bishiyoyi koraye fatau. Daga gefen ban d'aki ga wani mashinnan a ajjiye, k'irar roba_roba.Cikin falon na lek'a ta taga.Wata mata na gani zaune a kan doguwar kujera, kusa daf da wani babban mutum. Kallo d'aya nai musu na gane mata da miji ne.Pepopi ne ratata a gabanshi, na y'an makaranta yana yi musu maki.Ita kuma tana gefe tana d'an yi mai hira jifa_jifa. Kai kawai yake kad'a mata, halamun yana sauraronta. Yana yi yana kurb'ar shayi."Kaga fa mai martaba. Har yanzu yarannan basu shigo ba. Karfe biyar yanzu har da d'oriya. Ko ina suka tsaya?Kallonta yayi da zaratan idanunshi. Ya ce da'ita." ni kaina tunaninsu nake ta yi. Ga uwata ba ta son sanyi, ko ni bazan so ruwa ya daketa ba, kodan lalurarta ta asma. Amma bari na gani zuwa da rabi, in dai basu shigo ba sai in bi sahunsu. Ko, gimbiya?Murmushi suka sakarma junansu mai sanyin dad'i.K'ofar gidan su ka jiyo ana kwankwasawa, tare da jiyo sallama. Yayi daidai da b'allewar ruwan saman.Da hanzari ya mike."Bari inje, na ji ana sallama.Fice wa yayi da d'an gudu, zuwa k'ofar gidan. Wani mutumi ya gani tare da wata mace, har sun soma jik'ewa." kune kuke sallama? Bismillah ku shigo daga ciki."Malam mun gode amma tambaya mu ke yi. Gidan Malam Iliyas malamin babbar makarantar gwamnati.Dubanshi yayi da kyau. Tabbas bai gane shi ba, amma gashi ya ambaci sunanshi." bismillah ku shigo. Ni ...
App exclusive
Continue “UWA ALJANNAR DUNIYA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.