FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Part 1
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 ✨ *_JALALA_* ✨💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah) *_The writer of_*-Sauyin Rayuwa.-Nasmah ko Nasirah.-Sara da Sassaqa.-Indo a Birni.-So Bai San Jini Ba.-Ruɗanin Zuciya Biyu.-Akan Ƴar Uwata.-Doctor Hassan.-Gelle Ɓingel.-Ƙauyenmu.-Hatsabibiya Saude.-Aminaina ko Ita?.-Ƙullalliya. ALHAMDULILLAH TSARKI YA TABBATA GA UBANGIJIN DA YA HALICCI SAMMAI DA ƘASSAI, YA HALICCI MUTUM DA ALJAN YA YI WUTA DA ALJANNA, SARKI MABUWAYI WANDA BASHI DA KISHIYA BAI HAIFA BA BA'A HAIFESA BA, YANDA NA FARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA INA ROƘON UBANGIJI DA YASA NA GAMA LAFIYA *_Special tnx to my people, masoya masu ƙaunata a ko yaushe yauma dai gani da sabon salo mai tafiya da zamani, labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi da dama, ku kasance dani a cikin wannan labarin._**_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻Part 1 KWARA STATE. IFELODUN local Government IYABO QUARTER'S NEAR OMUPO WORD"Sauyin rayuwa kan nuna maka alamun ka hankalta, amma ina mamakin mutane da basa gane azancin duniya, duniya tamkar waina ce dake bisa kasko takan iya juya mutum a duk sanda taso, shiyasa ko yaushe nake fatan Duniya ta muku juyin alkairi, domin bana fatan abinda zai shiga tsakanin ku har ya samu damar rabaku tamkar jinina haka nake jinka *_NAMEER_* so nake ku kasance tsintsiya maɗauri ɗaya har ƙarshen numfashinku, *_HISHAM NAMEER_* ba iya Amini yake a wajen ka ba tamkar ɗan uwa na jini haka yake tunda a hannuna ya tashi tun bayan mutuwar mahaifansa, Soyayyar ku da abotarku tun ta yarinta ne, duk da a zuciyata bana jin akwai abinda zai iya rabaku saboda tsantsar ƙaunar dake tsakanin ku, amma wasiyya da nasiha ta dole ce a gareku, abotarku tana da ƙarfin da tafi jini tasiri, nasan dole ne kuyi nasara akan maƙiyanku ina matuƙar alfahari daku ina muku wannan nasihar ce saboda ita mutuwa bata da notice haka kuma bata ƙwanƙwasawa bawa ƙofa, zan iya komawa ga mahallicina a ko wani lokaci." Kallon Nameer Hisham yayi tare da sakin numfashi yace. "Abba Ina mantawa da cewa Nameer Abokina ne, kallon jinana kawai nake masa, yana kyautata min Abba, yakan yaƙi da duk wata damuwar da yaga ta tunkaro ne, karka manta Abba, Ammi ta kasance ta bamu tarbiyya iri ɗaya, ta bamu abinci a baki tare, ta share mana hawaye tare, to ta yaya zan ɗauke sa iya Aboki kawai? ya wuce wannan matsayin Abba, domin ƙaunar da nake masa ta kai ga zan iya mallaka masa komai a rayuwata domin kuwa yafi min komai mahimmanci ina matukar alfahari da Nameer Abba shine jigon rayuwata na basa duk wata yardata." "Abba Hisham fa ɗan uwana ne ka daina shakku akanmu domin kuwa z...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.