FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci
Sample · Chapter one
JARIRAI*Lamarin ya fara ne a wata ranar Laraba da safe ina ta sauri dan fita aiki, kasancewar a ranar ina da wasu manyan ayyuka da zan gabatar.Ina Toilet ina murza wanka da injin Bature mai tunkuɗo ruwa, (Shawa), kamar almara kunnuwana suka fara jiyo min sautin kukan *JARIRAI* daga wajen ɗakin, nan da nan na dakata da murza soson wankan da na ke yi a jikina nayi tsai! Ina sauraro dan tabbatar da saƙon da kunnuwan nawa suke aikewa da ƙwaƙwalwata.Da gaske dai kukan *JARIRAI* ne na ke ji, Ras! Ƙirjina ya buga da ƙarfi, ba komai ne kuma ya saka ni cikin wannan yanayin ba face sanin da nayi cewar Matata ko ɓatan wata bata taɓa yi ba tsawon shekaru bakwai da yin aurenmu balle in saka ran ita ce cikinta ya tsufa ta haife shi yanzu-yanzu.Kukan Jariran ya cigaba da ratsa dodon kunnena ya na ƙara hauhawar min da farashin faɗuwar gaba.Nan da nan nayi jifa da soson wankam na shiga ɗauraye jikina bab...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.