MIN QALBFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

MIN QALB

  • 1views
  • 18chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writer👈

More from @mamuhgee

Sample · 1

*_MIN QALB_*_Mamuhgee_1Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo ya zubar a babbar bolar bakin anguwar wadda za'a Kira da qaramar kasuwa sbd hargitsi da cunkushewar anguwar da manya da qananan kwatocinda suke cike taf da ruwa da ledoji tareda qananan abinci na wanke wanke dasuke biyowa,Daukar biredin tayi tana kakkabewa tareda kaiwa bakinta daya gama bushewa yayi fari fat harya Fara yayyankewa alamar ko yawun bakinta sun gama bushewa ta gutsura kadan ta Dan tauna taji zai shiga Da sauri ta qarasa turasa cikin bakin tana taunawa da sauri jikinta na rawa tareda hanjinta dasuke qugin jin wani abu ya saukar musu bayan kwanaki dasuka Dan dauka a na'de.Ganin wani almajiri yayo gurin Yana kallon biredin a yunwace Shima Dan ko gabansa baya kallo idonsa nakan biredin ko kyaftawa bayayi yasa tayi saurin miqewa tana qara tura biredin cikin bakinta da sauri sauri tana kallon almajirin karya iso gurinta Bata cinyeba ya kwace sbd wannan shine Abinda yake faruwa a bolar qwacewa daga marasa qarfi Wanda a duniyarma hakane duk me qarfi shike qwace Abinda yakeso gurin masashi,Batada uwa batada uba,Batasan kowa aduniyaba Wanda zata ce nata ne,Ita aduniyarma gaba daya batasan komaiba face yawon bola da tsince tsince.Almajirin na isowa gurinta yayi wuf da qarfi ya qwace biredin hannuwansa na rawa Shima yakai bakinsa yanaci da sauri sauri Yana hadiyewa ko taunawa bayayi sbd sauri yakai bakinsa.Kallonsa takeyi tana hawaye tana lashe sauran Dan gari garin biredin dake hannunta tareda uwar dau'dar dake tafin hannuwan nata dasuka sauya kala sbd dau'da.Tana kallo ya cinye biredin ya dago Yana kallon hannuwanta ko zaiga wani abin naci sbd yunwar dakeci hanjinsa yakai ko numfashi baya iyayi ko mushe yagani zai iya ci sbd qarfinsa daya gama qarewa gurin yawon bara.Ganin yanawa hannuwanta kallon yunwa yasa ta juya ta tafiyarta zuwa tsakiyar bolar tana bincikawa ko zata Kuma samun wani abin.Yarinyace qarama sosai Yar kimanin shekaru bakwai saidai yunwa da wahala Sunsa ta matse sosai kamar Yar shekaru shida,Dau'da tasa fatarta takoma baqiqirin ko tantance asalin kalar fatarta ba'ayi Ga gashin kanta daya gama tsinkewa sbd dau'da da zamansa a bude.Gangarawa tayi yafito cikin bolar tana qoqarin bude gwangwanin data samu cikin bolar fuskarta na nuna 'dokin son ganin me tasamo.Bakin shagon alhajiyat me abincin bakin titin ta zauna daga can gefe inda ake Mata wanke wanke ta faki idanuwansu ta dauki wata matacciyar butar tsarkinsu ta Dora baki tafara kwankwadar ruwan da sauri sauri wani sanyin rahama na sauka cikin hanjinta ita batamasan wani abu qazantar ruwanba burinta dai su sauka a cikinta.Fizge butar akayi da qarfi tareda jefarwa cikin masifa matar tasaka qafa ta tureta gefe tana cewa'"Wannan yarinya wlh anyi muguwar mayya,Yarinya saikace kafira...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters18
premium12
07

7

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
08

8

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
09

9

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
10

10 &11

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
11

12 & 13

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
12

14&15

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
13

16&17

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
14

18&19

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
15

20&21

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
16

22&23

Premium
Updated 5 months agoAvailable now
17

24&25

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
18

26

Premium
Updated 3 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play