MABUDIN ZUCIYAFree

ArewaPen original

FantasyFreeOngoing

MABUDIN ZUCIYA

  • 1views
  • 44chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Part 1

💕 _MABUDIN ZUCIYA_ 💕 *1*©®Hafsat RanoBismillahi rahmanirrahim, Alhamdulillah Ya Allah!***Da sauri-sauri yake motsa jikin duk ya hada gumi sosai, be tsaya ba sai da yaji ya gaji sosai sannan ya tsaya, da sauri Mudan dake bayan sa ya mik'a masa towel me dauke da tambarin wata tsuntsuwa me kyau a tsakiya an rubutu RS da babban baki. Karba yayi ya goge fuskar sa zuwa saman wuyansa, ya kafa robar ruwa ya shiga sha a nutse har ya shanye tas. Jefar da robar yayi a wajen ya saki towel din ya zame ya fadi a kasa, ya juyo ya hade hannaye sa yayi yayi wata alama.."Just 20min."Ya fad'a yana barin wajen da sassarfa. Bin bayan sa Mudan yayi da tarkacen da ya bari a wajen.Toilet ya fad'a, ya sakar ma kansa ruwa yana fatan abinda yake ji a chunkushe a kirjin sa ya ragu ko da kankani ne, sai dai baya jin akwai wani abu da zai rage masa yadda yake ji din ko da kuwa kaso daya ne cikin dari na abinda ya danne dukkan wani farin cikin sa,wanda yake jin ba zai taba dawowa daidai ba. Haka ya hakura ya fito ya shiga shiryawa yana son gama komai a mintuna 20 din da yace. Ka'idar sa ce yin komai a cikin lokaci dan a ganin sa bashi da lokacin batawa sam, komai yana yin sa a tsare ne ba tare da wani ya shiga cikin wani ba. Mutum ne shi me matukar sauri da kazar-kazar a dukkan ayyukansa, amma kuma yana da nauyi sosai a a magana dan babu abu ma fi wahalaa wajen sa kamar yawan magana wanda a da idan ya fara magana sai kace yayi shiru idan ya samu yadda yake so. Sai gashi lokaci daya chanji yazo masa irin wanda be taba tunani ba. A tsaye ya tarar da Mudan a harabar gidan wanda ke dauke da gidaje hawa hawa masu yawan gaske, gidan na daya daga cikin jerin gidaje manya na masu fad'a aji a cikin birnin na Ikko Lagos state. Be wani bata lokaci ba ya fada motar Mudan ya ja suka tafi. Kai tsaye wani hadadden restaurant suka tsaya, Mudan ya fita jim kadan ya dawo dauke da manyan ledoji ya saka su a gefen sa sannan ya sake shiga suka bar wajen.*RSARINA TEXTILE INDUSTRY LIMITED* Kansa a kasa yana duba wayar sa har suka iso, ya dago a hankali ya kurawa rubutun dake saman ginin Ido kamar me son ganin wani abu, a zahiri kallon wajen yake sai dai a bad'ini abubuwan da suke tunkaro sa ne suke masa yawo akai, yana tuna maganar su ta karshe wadda ta zama kamar wani MABUDIN da ya bude masa duk wani abu da yake a rufe, idan yace baya shiga tashin hankali a duk sanda irin wannan tunanin yazo masa sai dai ya kan yi kokarin danne wa ko dan wadanda rayuwar su take karkashin sa. Da kyar ya sauke kafafunsa ya fito daga motar bayan Mudan ya bude masa kofa, ya jasu zuwa cikin ginin wanda ya kasance babban gaske. A hankali ya kutsa kansa ciki yana tafiya a nutse irin ta cikakken namijin duniya, duk inda ya wuce sai sun gaida shi, ya amsa kamar yadda ya saba musu kadaran kadahan, har ya dangana da bab...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “MABUDIN ZUCIYA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play