FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Army of BTS💜
Sample · 1
MADUBIN GOBE"Nuratu! Nuratu?" Hajiya Sadiya dake zaune bakin katifar ƴarta tana ƙiran sunanta lokaci ɗaya tare da yaye abin da ta rufe jikinta dashi.Motsi tayi har lokacin bata buɗe ido ba."Mami da sauran lokacin shan maganin, don Allah ki bar ni inyi bacci kaɗan, yanzu zan farka.""Ki tashi kisha ko in ɓata miki rai, tun ɗazu nake faman tashinki kin ƙi ji."Yaye abin da ta rufe jikinta dashi Nuratu tayi ta tashi ta zauna, tana mutsetstseke ido ta ce."Yanzu Mami bazan taɓa kwana na wuni ban sha magani ba, shikenan rayuwata haka za ta ƙare."Sauyin yanayi da ta gani a fuskar mahaifiyarta ya sata yin shuru, ta karɓi maganin hannunta da ruwa."Komai zai wuce Nuratu. Ƙaddarar mu gaba ɗaya kenan ba ke ɗaya ba. In sha Allah watarana za ki kwana ki wuni ba ki sha magani ba da yardar Allah. Ko kin manta me Dr Awwab ya faɗa."Girgiza kai Nuratu ta yi lokacin da ta saka ruwa a bakinta don kora maganin....
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.