FreeArewaPen original
HAYATUL-ISLAM
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Army of BTS💜
Sample · 1
"A sayi ruwa mai sanyi." Matashin saurayin ɗan shekaru ashirin da uku yake faɗi cikin tashar garin nasu, wanda yake cike da jama’a, cike da dukkan ƙarfin muryar shi da Allah ya ba shi ya ke fadin haka.Hannu da ya ga ake ɗago daga wani mota yasa da sauri ya nufi wajen motar, yana isa ya sauƙar da babban robar ruwa da yake kansa a cike, yana cewa. "Hajiya na nawa kike so?""Ba mu na hamsin ya ishe mu." Matar da ya ƙira da Hajiya ta faɗa mishi, ta buɗe jakarta ta ciro naira ɗari biyu ta miƙa mishi. Ta sake cewa. "Wannan zafin cikin motar ai sai ya gasa mutum kafin ya isa. Hadiri ne a garin nan, ni dai fatana kar ruwa ya tare mu a hanya ya mana mugun bugu." Murmushi kawai ya yi, ya kwashi pure water na daidai kudinta ya miƙa mata. Harara ta buga mishi ta ce. "Kai me haka? Haka zan riƙe a hannu ba ka da leda.""Yi haƙuri Tsohuwa." Ya ce yana ɗaukar leda ya miƙa mata, ta karɓa tana gunguni ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.