FreeArewaPen original
WANE NE SANADI
- 1views
- 20chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
*WANE NE SANADI*BYUMMU HEBBAT*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ```Assalamu alaikum yan'uwa ina muku Barka da wanan lokaci fatan kowa yayi Sallah lafiya ina mai farin cikin kasan cewa tare da ku a cikin sabon littafi na mai suna *WANE NE SANADI* wanda ada kuka san shi da suna matar aure da zina waye sanadi. Tom shine dai na sakaya sunan saboda kalmar zina babu daɗin faɗa abaki Ubangiji Allah ya tsare mu baki daya! Ameeen```_Wanna book ɗin nawa sadaukarwa ne ga wasu mutane masu daraja a guri na Na farko Akwai Ƙawar Alkairi sahibar zuciyata daya tamakar da dubu wato *Fatima Maiduguri* wacce jama'a suka santa da suna Ummu ramlat 🥰🧡ina miki fatan alheri a dukkan inda kike Ubangiji yabaki lafiya. Sanan akawai wata garkuwa ta aduniyar marubuta jajirtacciya ta wato *HAFSAT A GARKUWA* Allah ya biya miki bukatun ki na Alkairi wanan sadaukarwa ce agare ku_```Da sunan Allah mai rahama nake roƙonsa da ya aramin nisan kwana wajen ganin na rubuta wanan book ɗin nawa mai girman daraja ya ldda na fara Allah ya bani ikon kammala wa lafiya.```_*Ƙarƙashin ƙungiyata abin alfaharina wato WOMEN WRITER'S ASSOCIATION*_*Free page 01*...Humm wai ke dole ne sai an yabi kwalliyar ne ko kuwa farilla ne ? "A'a ko ɗaya inason ka gane wani abu My hubby ko ba komai idan kace yayi kyau zan ji daɗi fa."Ok tom! ki jima baki ji daɗi ba ya faɗa yana me ficewa a falon. Da kallo ta bishi irin na Allah ya kyauta dinnan.Bata wani jima ba ta na kishin gide a kujerar da ke falon janyo wayar ta tayi tare da bude data sakon farko shi yafara gigita ta! Ganin yadda yake sakin kalmomi kamar ba gobe . Sai da zuciyar ta ta firgita shin mai yake shirin faruwa da ita ne shiru tayi tana nazarin tex ɗin nashi chan taga hakan ba shi da amfani Agareta kawai sai ta miƙe takama hanya abin ta ta wuce tsaƙar gida domin cigaba da ayyukan ya. Ummu FADEEL kenan mata a gurin SHAMSUDDEEN.Misalin biyar na yamma tana zaune abakikn kofar kitchen tana tuƙa tuwan semonvita yayinda ta kammala da haɗa miyar ƙubewar ta mai rai da lafiya! Saurin ƙara sawa tayi abinta domin tana tunanin magrib ta kawo kai ita kuwa a ranta bata son aikinta ya Kai ta dare chan naga ta shiga ɗakin dake da ke kusa da wanna kitchen din tafito da wani kosko na turare wuta ta ɗiba abinta takai tasanya turaren wuta kafin kace me tuni gidan ya dau kamshi kamar gidan amarya ! Haka ta zo ta kammala wannan girkin ta juya komai abinta kai kace batayi girki agurin ba tsafta dai kam akwata agurin wanna baiwar Allah fiddausi kenan manyan mata hankali kwance tayi saurin shiga wanka bata wani jima ba ta fito abinta kamar zinariya sai kyalli take bayan mintuna kaɗan naganta sanye da wani kyakkyawan shiga na tamfa ɗinkin riga da siket ta sha kamshi ta ko ina abinta tunani na zanga tayi saurin shimfit ɗane a ...
App exclusive
Continue “WANE NE SANADI” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.