GIRMA YA FADIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

GIRMA YA FADI

  • 1views
  • 7chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1 (Farko)

KAUYEN GWARZO, 1988Sunan da na taso da shi tun ina karama shine Zaynab Aliyu Gwarzo. Asalin mahaifina mutumin garin GWARZO ne da ke cikin jihar Kano da ake kira Malam Ali Mai Almajirai. Malam Ali, sananne ne a ciki da wajen kauyen Gwarzo da ya shahara wajen ba da maganin cututtukan da suka shafi aljanu daga Alkur’ani mai tsarki. Bayan magani da yake bayarwa yana karantar da dubban almajirai, kuma fitaccen manomi ne, makiyayi. Ya mallaki manya-manyan gonaki guda biyar, tirken dabbobi zuwa tsintsayen gida irin su kajin gidan gona, agwagi, talo-talo, jimina, gada, zabbi, akuyoyi da sauransu. Haka nan Malam Ali mutum ne mai cikar mutunci da tsananin kyauta, duk wanda ya kwana ya tashi a garin Gwarzo ya san da hakan. A garin Gwarzo baki dayanta Malam Ali fitacce ne da ake matukar girmamawa gami da ganin kima da mutuncinsa. Daga inda duk ka ce kana neman gidan Malam Ali, za a ce da kai “Mai Almajirai?” Daga ko’ina a cikin garin Gwarzo za a rakoka har dakalin gidan Malam Ali Mai Almajirai. Matan Malam Ali na aure uku ne, amma cikinsu babu wadda Allah ya baiwa haihuwa sai uwargida Inna Dubu da ta haifi Umar-Faruk shi kadai ya tsaya. Sai da ta yi haihuwa tara duk mutuwa suke tun suna jarirai wato (wabi). Daga Inna Dubu sai Inna Rakiya, sannan Innata,Rabi. Rabi matar Malam ta karshe Buzuwa ce fara sol, ita ce mahaifiyata kuma a hannunta na taso. Asalin auren Innata da Malam ya samo asali ne daga kawo ta neman magani, kasancewar Malam mutum mai ta’ammali da mutane daban-daban daga ko’ina cikin kasar Hausa da kewayen ta, manyan ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan boko da manyan ma’aikatan gwamnati kan zo neman taimako wajen sa a kan harkokin su, kuma suna ganin nasibi na hakika cikin taimakon sa, daga garuruwa daban-daban ana kawo marasa lafiya wadanda ya ware musu sashe guda a gidansa. Ya kan bada lakani na kasuwa, cututtukan da suka dami bil’adama, musamman wanda ya shafi aljanu zuwa cututtukan yau da kullum. Hakan ne yasa kullum za ka ga kofar gidanmu cike da motocin zamani wannan ya shiga wancan ya fita. To hakan ce ta hada shi da Alhaji Sani Buzu, shahararren dan kasuwar fata kuma dan siyasa daga garin Yamai ta kasar Niger. Ya zo Kano ne musmaman domin nemawa ‘yarshi maganin tabin aljanu da ta samu,tare da kanwarta Nuratu. A cikin Kano ne ya samu labarin Malam Ali ta hanyar wani abokinsa dan kasuwar Niger zuwa Kano, wanda shima ya sha zuwa amsar taimako hannun Malam Ali. Alhaji Sani bai san kowa a Kano ba, karewa ma ko zuwa bai taba yi ba sai a kan lalurar Rabi. Akwai kauna sosai tsakanin shi da ‘ya’yanshi biyu Rabi da Nuratu, wadanda mahaifiyarsu ta mutu ta bar mishi, tun rasuwar ta bai kara aure ba. Ya kawo su Rabi Kano da zummar neman magani ne kawai. Malam Ali, ba wai warkar da mahaukata yake ba, illa in lalurar kankanuwa ce ta kuma shafi aljanu bata gaga...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters7
premium5
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play