AMANA TAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

AMANA TA

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1 (Farko)

FARKON LABARIN Garin Dukku, dake cikin jihar Gombe, gari ne na Fulani masu asali da tushe, gari ne da Allah Ya yiwa albarkar kasar noma da ciyayin kiwo, Ya kuma azurta Fulanin wannan gari da shanu da tumaki masu albarka. A wannan lokacin za ki samu saurayi dan shekaru ashirin da biyar da garken shanu buka-buka nashi na kashin kansa, sai dai a wancan lokacin babu wutar nepa babu ruwan famfo a Dukku, sai dai albarkar rijiyoyi, fadamomi da koramu da Allah Ya bamu, dasu ne muke gudanar da al’amuran rayuwarmu na yau da kullum, cikin wadatar zucci da godiyar Allah. Ni da mahaifinki Umaru, ‘yan asalin garin Dukku ne, anyi mana aure tun ina da shekaru sha biyu. Aure irin na iyaye da kakanni, wanda babu sanayya ko wata soyayya a cikinsa. Ban sanshi ba, bai sanni ba, sai ranar da aka kai ni. Umaru dan sarauta ne a Dukku, mahaifinsa ke rike da sarautar San-Turakin Dukku. Fulani ne usul, wadanda suka gaji Sarautar San-Turaki tun daga kakannin-kakanninsu. Yayin da ni na kasance diyar talakawa, mahaifinshi shi ya nemi Babana Malam Sajoh da ya ba shi ni ya aurawa dansa Umaru, saboda kaunar da yake yiwa mahaifina, da irin tarbiyyar da yayi mana.   Zamani ne farkon zuwan boko, lokacin da duniya ke kwance; abin nufi, laifuffuka basu yawaita ba, haka boko bai fantsama ba. Sarakunan gargajiya sune suke mulki ba Gwamnati ba. Umaru da ‘yan tsirarun ‘yan’uwansa sune kadai suka samu damar yin ilimin boko a Dukku, yayin da Turawan wayar da kai suka kawo ziyarar wayar da kai fadar Sarkin Dukku. Umaru shi ya fara cewa zai shiga, suka bude makarantun firamare da sakandire wadanda basu samu goyon baya sosai ba daga al’ummar garin, musamman malaman addini, sai daidaiku irin su Umaru, da suke ‘ya’yan masarauta.                                                     Sunana Halimatus-Sa’adiyyah, mahaifina Malam Sajoh manomi ne mai rufin asiri, domin ya fi karfin abincin da iyalinshi za su ci, da sutturar da za su daura. Mahaifiyata Innayo, (Habibah), ta rasu wurin haihuwar kanina Bello. A lokacin ina da shekaru hudu, amma duk da karancin shekaruna ni ke kula da Bello, har zuwa lokacin da Baffanmu ya auri Inna Baddo, a lokacin ita ma mijinta ya rasu ba ta taba haihuwa ba. Don haka ta kama mu ni da kanina Bello ta rungume tamkar ita ta haife mu. Don haka zan iya ce dake ban tashi tare da mahaifiyata ba, amma kuma ban san maraici ba. Da zuciya daya Inna Baddo ke rike damu, har zuwa sanda mahaifina ya aurar dani ga mahaifinki. Rana ta farko da ya shigo dakina ya fada min cewa shi fa ba sona yake yi ba, saboda ni jahila ce, yana da wa...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium5
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated 3 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play