MASARAUTARMUFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

MASARAUTARMU

  • 1views
  • 8chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1(Farko)

          SHIMFIDARana ta tasamma faduwa, misalin karfe biyar na yamma. Lahadi ce, wadda ta kasance ranar kasuwar kauyen. Tsanyawa, karamar hukuma ce a cikin birnin Kano. A dai-dai wannan lokacin kasuwar garin ta fara watsewa, kowa na kokarin komawa gida cikin iyalin sa domin lokacin magariba ta kawo kai. Malam Hashimu, daya daga cikin dattijan garin Tsanyawa, dattijo ne mai kamala dan kimanin shekaru sittin da biyar, ya baro kasuwar akan keken sa, wani tsohon keke wanda da kyar tayoyin sa ke juyawa sabida tsatsa da tsufa. A hankali yake tafe a gefen hanya kikiki-kikiki....bayan keken sa dauke da tsarabar kasuwa ta kayan miya (kayan gwari) wadanda yake sayarwa da tsarabar yalo, dafaffen rogo da rake dasu agwaluma cike taf a katuwar leda. Tun daga bayan darnin gidan sa ya ke jiyo tashin kukan diyar sa SA'ADE. Zuciyar sa ta tsinke...kamar koyaushe ya ji kukan yarinyar tasa. Ya kara gudun keken sa ya iso gida jikin sa yana rawa, da hanzari ya jinginar dashi a jikin jinka ba tare da ya bi ta kan ledar tsarabar sa ba, ya fada gidan da dan banzan sauri, babbar rigar sa tana harde shi saura kadan ya fadi, da kyar ya samu ya dafa katangar dakin sa ya shigo gidan kamar an jefo shi.Abinda ya zata shi ya gani, wato mai dakin sa ce Inna Laure ke jibgar Sa'ade, da wani murtukeken iccen darbejiya tun karfin ta, yarinyar tana ta ihu da neman taimako kamar kullum. Hannu ya mika ya daga yarinyar wadda ke kuka kamar ranta zai fita tana fadin....."Baba ka cece ni Inna zata kashe ni....". Inna Laure ta yarda iccen tana masifa tana fadin. "Gobe ki sake dawo min da sauran gasara baki sayar ba, ki ga yadda zanyi da ke a gidan nan. Haka kawai ki dinga jaza min asara, ai ba uban naki ya bani jarin ba, in baza ki yi min talla ba, to ya dauke ki ya yi miki aure. Ba zan zauna ina ciyar daku ga banza ba, kartin banza kartin wofi da basu san komai ba sai ci da juyewa a masai, dole ki fita ki nemo min tunda kun zame min jaraba daga ke har sullutun uban naki da bai ko iya ciyar da gidan sa".Malam Hashimu bai ce komi ba, amma ba kalmar data fi bakanta mai rai cikin maganganun ta irin "sullutu", ya tada yarinyar ya kama hannun ta suka nufi dakin sa. Har zuwa lokacin Sa'ade kuka take yi jikin ta yayi birdin-birdin yana ta rawa.A gefen wata tsohuwar kujera kwalli daya da ke dakin mahaifin nata ta zauna, ta takure jikin ta tana sheshsheka hadi da hadiyar zuciya.Malam Hashimu ya ce "bar kukan ki gaya min kin ci abinci?"Sa'ade ta girgiza kai hawaye na sakko mata. "Baba tun kokon safe, ban kara cin komai ba".Tashi yayi ya koma inda ya jingine kekensa ya dauko kullin ledar da ya dawo da ita, ya dawo ya zauna a gaban 'yar tasa. Kwancewa yayi ya fiddo daurin awara mai zafi a cikin leda ya tura mata gaban ta ya ce "maza cinye".Sa...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters8
premium7
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated a month agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated a month agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated a month agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated a month agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated a month agoAvailable now
07

Book 4 (Farko)

Premium
Updated a month agoAvailable now
08

Book 4 (Karshe)

Premium
Updated a month agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play