FreeArewaPen original
ZUMUNTAR KENAN!
- 1views
- 8chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI
Sample · Book 1 (Farko)
Da ka doso garin Giwa gidan za ka fara hanga daga gabas masu kudu na garin, tangamemen gida da aka yiwa jan rufi na zamani mai zagaye da girgijejen gate na bakin karfe da aka fi kira da Mahdi-ka-ture. Dauke yake da (estate) guda wanda ya hadiye gidaje na zamani (flat) guda goma sha biyar. Idan ka daga kanka sama, rubutu ne da aka yi da ruwan gwal mai sheki an rubuta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ESTATE. Gidaje ne reras (dispersed) masu sanyin gani a ido da fenti ruwan gwaiduwar kwai. Gida daya ne ya bambanta da wadannan gidaje guda goma sha hudu wato gida na farko. Gida na farko ya fi duka gidajen girma, kuma shi kadai ne mai hawan bene. Mamallakiyar wannan babban gida tsohuwa ce ‘yar kimanin shekaru saba’in da biyar mai amsa sunan HAJIYA HADIZA GIWA, wadda ‘ya’ya da jikokinta ke kira da HAJJAH. Za ka yi mamaki idan ka ji cewa, duk girman gidan nan ita kadai ta yi rayuwa a cikinsa a matsayin ma...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.