A BARI YA HUCE...Free

ArewaPen original

RandomFreeOngoing

A BARI YA HUCE...

  • 1views
  • 8chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1 (Farko)

A BARI YA HUCE...-1 Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.   Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin. Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba. Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin.   Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa. Sana'arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya. Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana'ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba. Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana kan 'yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu.   Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe 'yar lelen ce zaune...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters8
premium7
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
07

Book 4 (Farko)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
08

Book 4 (Karshe)

Premium
Updated 6 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play