KULSUMFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

KULSUM

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1 (Farko)

           KULSUM 1Safiyar garin Lahadin yau ta kasance mai dauke da hadari bakikkirin, iska na kadawa da karfi, kamshin kasa mai dadi na tashi sakamakon dan yayyafi da aka fara, alamu ne na cewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci ruwa mai karfi zai iya sauka. Cikin tsakiyar watan Satumba, a cikin garin GAYA da ke cikin jihar Kano, a wata unguwa mai tsohon tarihi wai ita MAZA-GOMA. Sunan unguwar ya samo asali ne daga wata mace a shiyyar data haifi 'ya'ya maza goma a lokaci daya.            Gidan Malam Jibo, wanda aka fi sani da Baffa Jibo, sanannen gida ne a wannan unguwa, Malam Jibo mutumin kirki ne kuma manomi ne, wanda ya riki noma da daraja, ta kuma rike shi da iyalinsa cikin rufin asiri. Ya fi yin noman gyada, dankalin Hausa da makani lokacin rani. A duk shekara yana nome amfanin gona mai yawa, wanda yake sayarwa a nan cikin garin Gaya da makwabtanta ranar cin kasuwar kauyuka. Matarshi daya tun ta ladan noma, wato Aishatu da ake kira Goggo Shatu. Baffa Jibo (Jibril) da matarsa Aisha (Goggo Shatu) Allah bai ba su haihuwa ba sai a shekarun girmansu, shekarun su ashirin da aure kafin su samu haihuwar Sugrah. Shekarun Sugrah goma sha hudu aka aurar da ita ga wani malamin makarantar sakandire a garin ‘Yalleman ta jihar Jigawa. Duka-duka shekaru biyu da auren ta zo haihuwar diyarta ta fari, ko fuskar diyar Sugrah ba ta gani ba Allah ya amshi ran ta. Malam AbdulHadi, wato mijin Sugrah, ya dauki jaririyar da Sugrah ta bari ya damka wa mahaifiyarsa Iyatu. Iyatu ta rike diyar tsayin shekaru biyar cikin tsananin kulawa, shi kuma Malam Hadi ya kara aure. A shekarar da ‘yar ta shiga aji daya na firamare Allah ya karbi ran Iyatu, Malam Hadi ya so ya ci gaba da rikon ‘yarsa a hannunsa, amma take-taken Lami na rashin tausayi da rashin kulawa ga 'Kulsumu' ya sa dole ya dauke ta daga gabanta ya dawo da ita wajen kakanninta na wajen uwa a garin Gaya, wato Baffa Jibo da mai dakinsa Goggo Shatu.   Rashin haihuwa da Allah bai wadata su da shi ba, da soyayyar diyar su Sugrah da bata yi tsawon rai ba, su suka taru suka haifar da soyayya mai tsananin yawa tsakaninsu da jikanyar su Ummu Kulsumu, daga Baffa har Goggo Shatu ba sa iya boye son da suke ma Kulsumu, wannan ya sa Kulsumu ta taso goyon kakanni, wautarta ta yi yawa, ga sokonci da tsokana, amma fa duk da haka Kulsumu na son karatu, daga na boko har na Arabi, komai na Kulsumu irin na mahaifiyarta ne, wannan ya sa suke masifar kama da Goggonta. Malam Hadi na zuwa duk bayan wata uku ya duba Kulsumu, duk da Baffa ya dauki dukkan nauyin rayuwar Kulsumu mahaifinta ma na iyakar kokarinsa a kanta, in zai zo sai ya dinko mata sabon kaya ko kala daya ne ya sayo mata sabon takalmi ya dinko mata hijabi, in tana son ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium5
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated 9 days agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 9 days agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated 9 days agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play