FreeArewaPen original
GISHIRIN ZAMAN DUNIYA
- 1views
- 44chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Babi na 1 -2
Shinfi'da📖Kano gidan cike ya ke dam da 'yan Uwa da abokan arziki, wanda su ka amsa gayyatar biki na, daga gari gari. 'Yan uwan mahaifina da su ka kasance su ne jigon bikin, kab 'dinsu sun halarci wannan biki nawa. Daga 'bangaren maza a waje 'yan daurin aure kuma, Kawu Sulaiman wan mahaifina shine mad'aurin aure na. An cika ma'kil a k'ofar gidan mu dan gudanar da wannan 'daurin aure. Ni kuwa ina cikin kawayena da su ka kasance manyan mata. Dan kab kawayena babu budurwa, daga matan aure masu yara, sai zawarawa. Kasancewar na samu jinkirin aure. Shekaruna talatin da biyar a duniya. Daga gari gari a ka halarci wannan biki dan na yi gayya sosai. Abokan aikina na asibiti ma duk sun hallara, kasancewata ma'aikaciyar kiwon lafiya, bangaren anguwar zoma. Farin cikin da na ke ciki a wannan ranar bai da abun misali. Sanye na ke cikin riga da siket na atamfar Soso, mai kalar green da wani ganye ganye mai ruwan madara a jikin atamfar, na yi kyau sosai, sai busa kamshin turaren humra na ke yi. Kawayena sai tsokana ta su ke ta faman yi. Aminiyata makociyarmu Amina ce ta shigo d'akin da mu ke ni da kawayena ta na haki. Dubanta nai da mamaki nace.Ke kuma lafiya ki ke ta haki kamar wacce jaki ya ka da ita?" Ba ta ce da ni komai ba, hannuna kawai ta ja, tare da kirawo kawata Hadiza wacce ta zo bikina daga katsina. Fita mu ka yi zuwa bayan gidan mu, in da akwai rangwamen taron mata. Ta ce da ni."Sadiya akwai fa gagarumar matsala a wannan karon ma." Murmushin ya'ke na yi, domun zuchiyata har ta gama yi mun hasashen abunda amina ta ke so ta ce."An fasa auran wannan karon ma ko Amina?" Murmushi na sa ke sakar ma Amina, amma cikin zuchiyata ci take da wuta babababah. Hadiza ta ce."Amina dukkan mu ba yara bane. Ina tunanin kwakwalwarmu za ta iya shanye komai. Ki sanar da mu abunda ke faruwa." Yawu Amina ta ha'diye ta mi'komun wata kalanda. Hannu nasa na amsa jikina na rawa. A hankali na warware wannan kalandar. Abunda na gani shi ya tsananta bugun da zuchiyata ta ke ta faman yi, take hawaye su ka gama wanke mun 'yar fuskarta. Kalanda ce mai d'auke da hoton Ahmad mijin da zan aura yau, tare da kawata Fatima. Ko da na duba date sai na ga the same date da nawa daurin auren yau. Amina na duba na ce. Ina ki ka samu wannan kalandar Amina, Ahmad d'in dama soyayya su ke yi da Fatima ban sani ba, tare zai ha'da ya aure mu ko kuwa ita ka'dai zai aura, ni ya fasa aure na?" Dukka Wa'dannan tambayoyin a gigice na jeroma Amina, cikin dimuwa da tashin hankali mafifici. Sau uku ana kawo sadaki na, ana fasa auran, sabida kawai na yi ilimin boko mai zurfi har ina d'aukar albashi daga asusun gwamnati. Amina jiki a mace ta ce."Maman mu ce, ta je bikin jiya. Shine aka rarraba kalandar, yau d...
App exclusive
Continue “GISHIRIN ZAMAN DUNIYA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.