FreeArewaPen original
RAGAYAR DUTSE! COMPLETE 1,2,3,4
- 1views
- 29chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · CHAPTER 1
Maeken falo ne mai ɗauke da ƙayatattun kayan alatu na alfarma, fentin ɗakin baecin fari ne da shuɗi watau (blue and white), gadon kansa shuɗi ne da fari hatta zanin gadon da bargon duk fari ne da shuɗi. Dardumar dake kusa da gado shima fari ne da ratsin shuɗi, haka ma tayils ɗin dake malale a ƙasa, hatta labulayen dake sagale jikin bango suma fari ne da shuɗi, kai kusan komai na ɗakin launi biyu ne a ciki. Wannan haɗakan launikan ya Ƙarama ɗakin ƙayatuwa. A wannan makeken gado, Karimah ce kwance ta na sharara barci.Karimah shekarunta kusan talatin da takwas. A ƙusurwar ɗakin kuwa, mai gidan ne a zaune bisa kujera Ya ɗora laptop akan tebur ya na bitar aiyukan da Karimah ta tura ma sa na kamfaninsu. Lokaci zuwa lokaci yakan ɗago kai ya kalleta, wani lokaci ya yi murmushi wani lokaci ya yi ma ta kallon tausayi. Shi kuma mijin shekarunsa arba,in da biyar. Cikin haka ya tsinkayi ƙarar wayarsa, ya ɗauka ya duba sai ya nufi falo."haba Murja me kikeyi har yanzu ba ki barci ba? " acan ɓangaren aka Fara shashshekan kuka, "dakata! Mene ne abun kuka?" akaci ga ba, da kuka ana faɗin, "tun tahowarka banda Lafiya, ko ina ciwo yake mun a jikina, sannan komai naci sai nayi amai."Kin kira likita? Me Yace? ""wai ciki nake dashi.""Masha Allah, Alhamdulillah! Zan taho gobe Insha Allahu, idan kuwa ban samu jirgi Abuja ba, to Sai jibi in Allah ya Kai mu ko kuma in biyo mota. Ki Lura da kanki."Ya kashe wayar Ya na hamdala, amarya ta na da juna biyu, hmm! Wani hani ga Allah baiwace. Daya koma cikin ɗaki Sai ya tadda karima ta na ta bige bige haɗI da watsi da fulillikan gado, ya yi tsaye shiru ya ga gudun ruwanta. Sai kuma ya ga ta koma barci, ya yi ɗan murmushi yajuya zai koma ga kumfuta, Sai kuma ya fasa. Ya zo ya tashi Matarsa don suyi sallah. "tashi muyi salla" zumbur ta tashi da yake ba ta da nauyin barcin, ta share fuska ta na faɗin."Bana sallah.""Eh to, tashi dai Ki ɗauro alwala sai kiyi azkar a zaune." suka faɗa bayi tare. suka ɗauro alwala, ta ɗora dardumar sallah bisa kafet ɗin jikin gado kana ta saka hijab ta zauna ta Kalli gabas ta Fara jan carbi, shi kuma ya fara salla, sun ɗauki dogon lokaci su na ibada har aka Kira sallan subahi. Al,amin a gida ya yi sallarsa ta subahi, daga nan Kowa ya ɓingire anan wajen. Hakan ya ja masu makara don basu farka ba Sai wajen ƙarfe tara, ƙarar waya ce ta tashi karima, ta yi firgigi ta rarimo wayar. Zahirah ce a layi take faɗin, "Hajiya ku tashi mun makara." Karima ta isa ga mijinta ta girgiza shi, wuf! Ya Miƙe ya faɗa bayi. &n...
App exclusive
Continue “RAGAYAR DUTSE! COMPLETE 1,2,3,4” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.