FreeArewaPen original
Da Na Gaba...
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Broadcast Journalist/Writer/Blogger/Social Rights Activist
Sample · NA ƊAYA
Pam, na zaune a ƙarƙashin babbar bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gonar sa. Ya harɗe ƙafafunsa, ya ɗauki ƙoƙon burkutun da ke gaban sa ya kafa kai yana kurɓa.Jim kaɗan ya ɗago kansa ya yi wata gyatsa tare da yamutsa fuska, ya ajiye sauran burkutun da ya rage a gefe, yayin da ya ji wata zufa ta keto masa. Wani sanyi ya ratsa gadon bayansa saboda wata iska da ta kaɗa, sakamakon wani hadari da yake shirin haɗuwa.Lokaci ne na tsakiyar damina, don haka ana samun ruwan sama sosai yanzu. Pam ya yi tunani a ransa, lallai lokaci ya yi da zai tashi haka ya tafi gida, mai yiwuwa matarsa Kaneng ta dawo daga kasuwar da ta ce za ta je cefane, domin kuwa yamma ta fara yi, kuma ga garin yana rufewa.Ya miƙe tsaye ya fara karkaɗe ƙasar da ke jikin sa.Pam, matashi ne da ba zai wuce shekaru talatin da biyar ba. Baƙi ne kakkaura, ba shi da tsayi sosai. Magidanci ne da yake da iyali, matarsa Kaneng da y...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.