AL'AJABFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

AL'AJAB

  • 1views
  • 21chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

A wife,a mother,a friend,a dreamer and lastly but not the least,a writer with a new perspective😁😘😘😘

More from @oumwalid

Sample · Chapter :1

*AL'AJAB* by 🌹 OUM WALID KD🌹*Page 1* Daukacin ilahirin al'ummar dake da matsuguni ke kuma rayuwa a SODANGI ESTATE idan kacire yara yan ƙasa da shekaru goma sha takwas babu wanda bai halarci wannan taron ba,taro ne wanda yasha bamban da sauran taron daya zame wa mutane SODANGI ESTATE al'ada wacce suke yi a kowace farko ko karshen shekara,ko wanda suke idan zasu yi haɗin auratayya a tsakanin ya'yansu wanda duk tushen su ɗaya ko wanda suke yi domin kawo gyara a cikin zuriyartasu. Wannan taro na yau cigaba ne daga wacce suka yi ajiya wanda shine zama na farko wuni suka yi inda aka yita kokarin warware tsarkakiyar da mutane uku suke ciki amma haka aka tashi ba tare da an samo bakin zaren ba, wannan shine zama na biyu, taron yazo musu ne a ɓagatatan babu zato babu tsamani balle kuma ayi batun shiri, domin kuwa ko wata biyu beyi ba da aka watse daga wancan taron wanda hakan na nufin suna wata na biyu ne cikin sabuwar shekara wato fabrairu,ba kuma sun haɗu bane dan haɗin auratayya a tsakanin ya'yansu ba,babu me ciwo ko me buƙatar jari babu kuma masu bukatan sasanci ko alkalanci, ta wani bangaren ana iya cewa lallai zaman alkalanci akeyi dan wannan taro daidai yake da zaman kotu.Katafaren falon cike yake maƙil da mutane maza da mata,yara da manya iyaye da ya'yansu wasu harda jikoki,wasu a tsaitsaye wasu sun zauna yayinda wasu suke a rakuɓe a gefe duk wanda ya gansu yasan daga tsatso ɗaya, tushe ɗaya kuma zuriya ɗaya suka fito domin kama da juna da suke,akasarinsu farare ne sol sol amma hatta da baƙaƙen cikinsu kyawawa ne ga uwar hanci duk wanda ka kalla sai hanci zirrr kamar biro.Zaune akan doguwar kujera three seater wani kyakkyawan farin tsoho ne wanda gashin kansa dana fuskarsa suka saje suka koma fari fatt kamar takarda saboda furfura domin kana ganinsa kasan an sha miya dan a shekaru ya baiwa dari baya amma kudi da hutu sun sanya ake masa kallon wanda shekarunsa ba zasu haura Tamanin ba(ALHAJI USMAN SODANGI,tsoho me ran karfe kenan) sanye yake da bugaggiyar shadda fara karrr kansa farin hula ne da kuma nadin farin rawani,gefe da gefensa ya'yansa maza ne su bakwai suma zaune akan kujeru,tsaf kana ganinsu kasan fuskar ubansu suka dauko sai babbar yarsa wace take zaune a kasa kusa da kafan mahaifin nata na hagu yayinda daga damansa kyakkyawar matashiyar yarinyace baka yar kimanin shekaru sha takwas wacce kallo daya zaka yi mata kasan lallai tana cikin matsananciyar damuwa maras misaltuwa kuka take mara sauti sai hawaye dake kwararowa daga idanuwanta,babu wanda yayi yunkurin hanata domin su kansu manyan nata suna cikin damuwa da rudani,gabaki dayansu alhaji babba suke jira domin ya bude taron da addu'a daga nan kuma a samo maslaha wa wannan gagarumin al'amari daya kutso kai cikin sodangi estate, duk da ya'yan nasa sun manyanta dan cikinsu babu wanda ba...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters21
premium17
05

Chapter :5

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
06

Chapter :6

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
07

Chapter :7

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
08

Chapter :8

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
09

Chapter :9

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
10

Chapter :10

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
11

Chapter :11

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
12

Chapter :12

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
13

Chapter :13

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
14

Chapter :14

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
15

Chapter :15

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
16

Chapter :16

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
17

Chapter : 17

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
18

Chapter : 18

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
19

Chapter : 19

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
20

Chapter : 20

Premium
Updated 4 years agoAvailable now
21

Chapter : 21

Premium
Updated 4 years agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play