FreeArewaPen original
ƘADDARATA SANADIN HASKE
- 1views
- 53chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
💕 **ƘADDARATA* *SANADIN* *HASKE* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM*_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼**🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```*** ``` *Free* *pg* *LAGOS* Tunda aka tsayar dasu a cikin cunkuson ababan hawan take ta zabga tsaki tamkar zata tsinke harshenta, Muhsin dake gefanta a cikin a daidaita ya juyo tare da zabga mata wata ƙatuwar harara,bai dai ce mata komai ba, ya juya ya cigaba da kallon motocin da suka zama sanadin cunkuson dake faruwa a halin yanzu,tsakin da ta kumayi akaro mara adadi shine abinda ya kuma fusata shi ya juyo afusacen tare da nunata da yatsa,wallahi Fahrin idan kika sake min tsuka cikin kunnuwa sai na tsinka miki mari, dame kikeso naji?da wannan jiran da kafuran nan suka haifar mana ko da tsakin ki?haba!" ya faɗa cike da kufula,ita ko yarinyar da aka kira da Fahrin murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tayi,tana gunguni aciki ba tare da ta bari sautin ta ya fito ba gudun kar tasha mazga gurin yayan nata.Daga can waje kuma kan babban titin Lagos ɗin, cike yake da zafafan motoci wan da gaba daya manyan pastoci ne tare wasu manya daga cikin mabiya addinin yahudawa, wasu tafe suke a ƙafa wasu a mashina,kana ganin su kasan cewa suna cike da farin cikin wannan rana,wata danƙareriyar mota ce tafi jan hankali na, wadda na kula daga dukkan alamu wanda yake cikin motar baƙaramin ƙusa bane ko kuma wani me muƙamin ko dai daya daga cikin manyan pastocin da ake ji dasu ,tun da gashi dai gaba ɗaya alamu sun nuna hakan , duba da yadda naga jami an tsaro sun da baibaye gaba da bayan motar,dana mota dana ƙasa kowa kaffa kaffa yakeyi da abinda zai rabi motar bare akai ga na cikin motar.Cikin wata irin murya me cike da sanyi da kuma yar tsiwar da ba wani iya ta tayi sosai ba, tace"wai dan Allah meke faruwa ne yau a garin nan?ko shugaban kasa ne zai wuce shine ya samu rakiyar ƴan maula? Fahrin ta tambayi me nafef ɗin,a dai dai lokacin da wani ɗan saurayi yazo shigewa ta gefan nafef ɗin yaji tambayar da Fahrin takeyi,dan haka tsalam sai ko ya shiga bata amsa da cewa,ai yaron pastor Matthew,,,aka bawa muƙamin pastor shine suke ta celebration kasan cewar sa yaro matashi da a wannan shekarar ya fara riƙe muƙamin fastor ne yasa abun ya Dada arna shi san nan kuma yaro ne uban talakawa Br BENJA ke kowa da ka gani san sa ya ke yi musulmi da kafuri kasancewar sa me gaskiya a fagen aikin sa mai kuma taimako talakawa na sane me kudi ma na sa ne in ɗai yana da gaskiya mai riko da addinin sa ne shi yasa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.