FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · CHAPTER 1 BIRI YA YI KAMA DA MUTUM.
WUKAR FAWA BABI NA DAYANa tashi zaune da kyar Ina dube-duben dakin, kantoci hudu na gani, a kowane kusurwar dakin. Kantar kusurwar gabas cike yake da littafan addini, yayinda kantar yamma ke makare da nau'ikan magungunan musulunci, kama daga Zaitun, habbatul sauda, man hulba, man tafarnuwa, na'a-na'a, ruwan kal, har da su shayin aljanu da turaren aljanu gasu almiski.Lallai duk wanda ya shigo dakin nan mudin ya na da aljanu, to kuwa sai sun fallasa kansu, domin da zarar ka shiga dakin za kaji wani irin kamshi ya dakin hancinka, to daga nan za ka fara ganin jiri.Ko yanzu jiri ne ke dibata, na runtse ido na bude inda naga mutane uku sanye da jallabiya sun zagaye ni, ko wanne su rike da alkur'ani. Na duba jikina na ganni sanye da riga da wando hadi da hijabi duk na Atamfa. A tsakiyar dakin kuwa, taburi ne dauke da katon rediyo ya na fidda karatul alkur'anil Kareem. "Sannu, ya ya ki...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.