NI DA KISHIYOYINAFree

ArewaPen original

ActionFreeOngoing

NI DA KISHIYOYINA

  • 1views
  • 20chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Am not just to here to write but to entertain and touch the heart of the readers

More from @sadnaf

Sample · Part 2

*NI DA KISHIYOYINA*      *NA SADNAF**E.W.F**PAID BOOK**BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*  *Page 2*LUBAMutane da dama suna ganin na aikata abin kunya nayi abin fade naci amana Wanda ni banga aibun abinda nayi ba tunda a musulunce ba haramun na aikata ba so so ne amma san Kai yafi,Ina san Jin dadi a rayuwata Ina san duk abinda nake so a rayuwata ya zama na samu,kina mace Ina mace ba abinda zaki gaya min Ina so naga na Zama mowa a wajen mijina ya zama ba matar data isa ta hada kafada dani Zan iya kashe ko nawa ne,Zan iya zuwa Ko'ina Ina dan na samu cikar burina.WaiwayeAisha Zuciyata cike take da farinciki dawowar da uban yayana zaiyi. Ya shafe shekara biyar a waje  dan ya Karo karatun da yana dawowa zai zama cikakken likita Allah yasan nayi kewarsa Kamar na mutu Ashraf da Afrah ma sai murna suke Abbansu zai dawo,nasan ashraf da wayonsa a lokacin da ya tafi yasani Afrah ce dai take da shekara biyu lokacin daya tafi.Salisu bashida komai a lokacin da mu kayi Aure dan zan iya cewa auren gata aka masa nima da yake a wajen yayana nake Yana kuma da dan rufin asiri Ina gama secondary school ya nemi salis daya fito da a lokacin ba wani aiki yake ba sai wani karamin chemist da yake dashi,da taimakon iyayen sa dai ya turo kudin aure gidanmu aka sa mana Rana wata shidda masu zuwa.A lokacin cikin tsananin farinciki salis ya bugo katin engagement na raba wa kawayena,a lokacin banida aminiya sama da Luba da a lokacin makaranta daya muka yi jinin mu ya hadu da ita sosai ba Wanda baisan kawancen mu ba, har ana mamakin yanda akayi tamu tazo daya da ita dan ni Sam bana San hayaniya ita kuwa akwai zuciya da fada gata masifafiya masifarta yasa lokacin samari ma basu fiye zuwa wajenta ba.A ranar da na bata labarin salis ya kawo kudin aurena mamaki ta ringayi tana mai salis yake dashi da zan aureshi ita har yanzu bata ga kalar Wanda zata aura ba.Dariya na sa mata ina nidai Ina sansa luba ni dama nafiso na auri Wanda bashida komai idan munyi aure mayi arzikin tare.Anan ta hade rai Wai taso muyi aure rana daya bazata so na rigata aure ba cikin dariya nace ta bada himma nan da wata shidda ta samo mijin aure ta tab'e baki tana ita dai taga Kamar nayi gaggawa.A kwana a tashi ba wuya sai gashi mun fara kirga sattikan Aurena,duk wani shiri da Luba muke yi dan itace gaba wajen fito da anko duk da ba wani shiri take da salis ba amma da ta ga dai shi zan aura ta fara sakar masa fuska a haka har aka sha shagalin bikina Luba tayi k'ok'ari sosai dan ba karamin gudunmawa tayi min ba haka ma a gidansu anyi min gudumawa na Kuma ji dadi matuka.Duk da na rigata aure ban canza mata ba,wai dan ganin yanzu ni inada aure hasali kawancen mu kara karfi yayi,dan ba abinda nake b'oye mata game da rayuwar Aurena itama b...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “NI DA KISHIYOYINA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play