SALMAFree

ArewaPen original

HorrorFreeOngoing

SALMA

  • 1views
  • 5chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

FATALWA BAƘAR TAFIYA SAKACI SALMA RAZANI WANI ƘARNI RUWA BIYU ƘULLALLIYA

More from @meenatyandoma

Sample · Part 1

👽 *SALMA* 👽    (HORROR STORY)     _NA MEEN@RT A YANDOMA_*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*       *M. W. A*```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ```🤙🏻*** Labarin Salma nina kirƙiri abuna, aguji juya mani labari ta kowa ce Siga sai da izinina.*NA KUƊI NE, KI TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KATIN MTN TA WANNAN NUMBER *****BANYI ALƘAWARIN YIN FREE PAGE DA YAWA BA, SABODA LABARIN NADA YAWA, HAJIYA KI BIYA KUƊI KISHA LABARI* 🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️*NA CIKA ALƘAWARI*👇🏻👇🏻👇🏻1\1\2022*FREE PAGE* *1️⃣__2️⃣*........Duhun dare ne mamaye da gari wanda ko tafin hannunka baka iya gani, gagarumin hadarin da ya yima garin ƙawanya ne ya ƙara haddasa ma garin matsanancin duhu,Tsawa gami da gagarumar walƙiya da aka fara ce ta haddasa ma Sahabi dake sheƙa gudu saman kwalta ƙara ba motar wuta.Walkiyar da aka yi ce ta sani taka birki babu shiri, iskane ya taso mai haɗe ga gagarumin ruwan sama.Gabas da yamma babu inda babu gida tsakiyar dajin Allah yake, jiyake kamar yayi kuka domin harga Allah ya tsani ruwan sama ya ta6ashi.Tsoki ya ja gamida fizgar motar.Gudu yake baya ko ganin gabanshi, sakamakon ruwanda ake sheƙawa kamar da bakin ƙwarya.Ba zato ba tsammani yaji ya kai ma wani abu karo.A matuƙar tsorace yayi nasarar taka murki.Bai san lokacin da ya buɗe mota ya fito a tsora ce ba duk da ruwan da tsalawa.Nai mai duniya yayi cikin ruwan nan amma bai ga koda wani icce ba dazai yi tunanin koshi ya buga.Ilahirin jikinshi a jiƙe yake sharaf, juyowa yayi da nufin ya koma mota.Caraf yaji anriƙe mashi ƙafa, a tsora ce ya kai dubanshi inda aka riƙe mashi ƙafar.Gagarumar walƙiyar da akayi ce tasa ta haddasa mashi hango wata mace tsugunne tana 6oye wani abu tayi mashi runfa da jikinta gudun kada ruwa ya ta6ashi.Cike da firgice yake ƙarema matar kallo, yarinyar mace ce bazata wuce shekaru ashirin da shida ba aduniya.Ɗago kanta tayi dake sunkuye gashin kanta ya rufe mata fuska.Tana ɗago fuskarta ana dallo wata uwar walƙiya.Ido suka haɗa da matar kanshi yayi wata mummunar sarawa, atake kwalwarshi taso ta tuno mashi wasu abubuwa da suka faru a baya amma yaji wani abu ya tokare mashi zuciya.Cikin kyarmar sanyi Matar ta buɗi baki ta fara magana."Sahabi! Nasan kaddara ta gama rubutuwa akanmu babu makawa hakan saiya faru, Sahabi nasan zakace waceceni amma kash ni kuma gashi na kusa shaƙar numfashina na ƙarshe."Tsaida maganar tayi tare da miƙewa tsaye da ƙyar ta fiddo jaririyar da ta guɗundune cikin wani zane.Shi dai Sahabi kallonta yake da matuƙar Mamaki."Saha...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters5
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play