FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Ina Alfahari da kasancewa ta Marubuciya
Sample · D'andano
*_MAHASEEM_* { ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }_NA_*_UMMU_ _BASHEER_*```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡{ _Home of Expert and Perfect Writers}_ ```Assalamu Alaikum Ina Kuke massoya littafan UMMU BASHEER, a yanzu tazo muku da Sabon labari mai d'auke da Nishad'antar, Ilimantarwa, Zumunci, Sadaukarwa, Tausayi tare da Tsantsar Soyayya,Zai zo muku cikin wani Sabon Salo, Litafin MAHASEEM na Kud'i ne 300kacal zaku biya Via Account ko Katin waya 300 na Airtel.``` ```Account NumberFatima AbdullahiAcc no 0592594133GT Bank``` Evidence of Payment ***Tun daga gate yake jiyo sautin kid'a dake tashi, ranshi a matuk'ar b'ace ya bud'e Parlour, Matar shi ce tare da Kawayen ta sun sa kida sai Rawa suke kwata kwata basu ji shigowar shi ba da alamu duniyar tayi musu dad'i, remote control ya d'auka ya kashe, A fusace ta juya tana cewa"Wani d'an iskan ne ya...." Maganar ta ne ya mak'ale Lokacin da ta ga Mijinta tsaye cikin b'acin rai."Kuna Hauka ne,gidan nawa zaku maida Club,Na baku one minute ku fita min daga gida kafin yanzu in kira Muku Police su tafi daku" Ya fad'a a tsawace. Jin ya ambaci Police yasa ba shiri suka kwashi jakunkunan su wasu ma takalma a hannu suka rik'e suka fita da gudu, Parlour'n ya Kalla ko'ina kaca kaca ga dati har throw Pillows duk zube a Floor, tsaki taja tace"Wannan ai rashin mutunci ne ya za'ayi muna jin dad'in Rayuwar mu da k'awaye na kawai ka wani...... " " Will you just shut up, are you Mad, Cikin gidan auren ki kike gayyato wa'inan y'an iskan k'awayen naki, lemme tell you bana son in k'ara ganin su a gidana" Ya fad'a with anger tare da shigewa bedroom din zuciyar shi na zafi, Yana matuk'ar k'aunar ta amma sam baya son halayen ta..... yana shigewa ciki taja tsaki"kayi kad'an Wallahi baka isa ka takura min ba ka hana ni huld'a da friends na mtsss"ta k'ara jan tsaki tare da D'aukar wayarta ta zauna ba tare da ta damu da ta gyara Parlour ba.********************************* zaune take kan Kujera kyakyawa ce, sanye da doguwar riga wanda yabi jikinta Cikinta ya fito yayi mata kyau,Tayi dauri ta d'an turo shi gaba tayi crossing legs tana tauna chewing gum tana d'an girgiza k'afar ta, time to time tana duba Wall Clock, Can taji an bud'e kofa, Sanye yake cikin Suit Maroon colour Kyakyawan saurayi, Kallon ta yayi da mamaki ganin bata taso ta tare shi ba yanda ta saba, k'arasa yayi ya ajiye ledojin hannun shi kan Dining Table sannan ya juyo ya kalle ta da alama rigima take ji, d'aure fuska yayi ya k'arasa gurin ta,tunawa da laifin da tayi mai. "Who gave You the right ki fita Compound kina rigima da wata cikin maza, wani irin rashin hankali ne wanann"ya fad'a cikin kishi. a fusace ta Mik'e dama kamar jira take fuska a d'...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.