FreeArewaPen original
Ya Abin Yake?
- 1views
- 14chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
✍️ Welcome to the World of Nazeefah Sabo Nashe ✍️ If you love emotional stories, family drama, secrets, betrayal, destiny, and unforgettable plot twists, then you’re in the right place. 📚 My Published Novels: 🔥 ƘWARYAR WUTA (Now Available) ❤️ Me Zan Yi Da Ita? 🤔 Ya Abin Yak...
Sample · Page 1
Kamar yarda ta saba tashin y’arta ta kullum, yau ma ranta a b’ace take shurinta da k’afa tana dukanta wai duk so take ta tashi. Da kyar Hamda ta bud’e idonta ta zuba su akan mahaifiyarta. Zazzafan zazzab’ine a jikinta amma hakan bai sa ta d’aga mata k’afa ba.Ta bud’e idonta da kyar da duk sun canja launi na azabar da take ciki, ba yau bane mafari haka dama can Ammin take tashinta daga barcin a kowace asubar fari, tamkar ba mahaifiyar da ta tsuguna ta haifota duniya ba. Duk da a kullum tana tantamar kasancewarta tsatson Ammin,saboda tsana muraran da take nuna mata, wanda ko ƴar tsintuwa sai haka a yarda Ammin take ɗaukar lamarinta.Hawayen idonta ya zuba akan fuskarta, da gaske tana jin ƙunar lamarin sau tari Mahmah da ta ksance kishiyar uwarta tafi lura da lamarinta fiye da Ammin koda kuwa a ɓoye ne don idan ta fuskanci ka na tausaya mata ma tsanarka take sosai ta kuma ja maka kashedi game da shiga shirgin yarinyarta.Da kyar ta miƙe zaune bayan ta dafa yaloluwar katifar ta irin ta ƴan boarding da take kwana akai ita ɗin ma tatace ta makaranta take kwana akai bayan gama karatunta. Hannayenta dafe da goshinta alamar kanta yana matuƙar sara mata ta ce "please Ammi wallahi yau da ciwon kai na tashi ba zan iya komai ba." haɗe rai tayi idanunta cikin nata tace "ƙwarai tunda yau kika saba aikin da ciwo a jikinki kin tashi ko sai mangareki?ai tunda kika sake kika zo duniya duk da ba ke naso haifa ba wallahi kin yi ta shan baƙar wahala kenan, ko kaɗan bana son na buɗe ido na ganki na tsaneki tsana mafi muni da ban taɓa yiwa wani ita ba, ki miƙe bakinki alaikum kije ki fara aikin da kika saba."Da kyar ta miƙe zuciyarta na wani irin hanƙaron ɓacin rai ta zuba idonta akan gadon da yake bedroom ɗin yayyenta ne zube su uku suna shan barcinsu akan gadajen da suke zube reras a cikin faffaɗan bedroom ɗin.. kuma duk babu wanda bai bata shekaru ba a Cikinsu babbar ta bata ak’alla shekara goma mabiyarta Ta bata shekara takwas yayinda wacce take bi ta bata shekaru shidda cif. Kuma duk ba suyi aureba. Yayarsu Najwa ce kawai mai aure a d’akin su. Hawayenta Ya sake ninkuwa fiye da nada, ta rasa me tayiwa Ammi da tayi mata wannan muguwar tsanar ga yayyenta nan zube bata saka su aikin ba sai ita da take ƙaramarsu, madadin auta da aka sani da riritawa ita mahaifiyarta wulaƙantata take tana kuma nuna mata tsana muraran da gaske bata sonta. Ta faɗa a gaban idonta ta faɗa a bayan idonta. Hasashe kala-kala tayi tana son gano dalilin tsanar sai dai sam bata ci ribar gane gaskiya ba.Bata Sani ba Ko don kasancewarta baƙa saɓanin su da suka kasance farare tas dasu don kalar Ammin suka ɗauko gaba ɗaya kasancewarta balarabiyar jordan, Gashinta yalolo suka ɗauko saɓanin ita da ta zamo kalar mutanen Habasha, Gashinta kuwa.cunkus yake ga taurin tsiya don ko kitsashi ba a iya yi, sau tari ha...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.