BAƘIN ƘULLIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

BAƘIN ƘULLI

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writer ✍️ Muslimah🧕 Physiotherapist 🧑‍⚕️ Daddy's pet 🌹 Momma's pride 🌺 My family is my happiness 💝

More from @ouummey

Sample · BAƘIN ƘULLI: 001

                 BƘ      FREE PAGE 1_________________________ SASA CENTRAL PRISON, SASA STATE, 11:40 am.Ihu da ta saki ne ya karaɗe ilahirin wajen, kuka take cike da raɗaɗi da azabar da take ji a jikin ta sanadin dukan da ƴan uwan ta masu laifi suka rufe ta dashi.Abu ne da ya zama kamar wajibi in har za'a fito dasu aiki to fa se ta sha kashi kafin ta bar wajen, hakan ke faruwa tun daga ranar da aka kawo ta gidan kason amma har zuwa yanzu da ta tasamma shekara a cikin sa ta kasa sabawa, a kullum abun sabo yake zame mata takawa sabo dashi.Bata san me ta tsare musu ba da suka yi mata irin wannan tsanar, kullum cikin ganin tayi ƙoƙarin kiyayewa duk wani abu da ze haɗa ta dasu take amma basa rasa samo abun da zasu ce tayi dan kawai su sami dalilin dukan ta.Duka ne suke mata cike da mugunta su kusan biyar akan ta, jibga jibgan mata ne manya da akalla wasu sun haife ta wasu kuma sun kusa haifar Tata suka zage karfin su suna nuna bajintar ƙwanjin su akan jikin ta, dunƙulewa tayi gefe ɗaya tana kuka tare da ƙoƙarin kare dukan sedai ina samun ta yake ko ta ina dan ba dukan hankali suke mata ba.Jinin dake zuba a bakin ta besa sun tausaya sun daina dukan ta ba dan ko a jikin su ma hakan be dame su ba da alamu so suke su fitar mata da wanda ya fishi dan sake dunƙule hannaye suke yi.Duk yadda yaso ya samu bacci ya gagara sanadin ihun dake shiga kunnen sa yana amsa amo a ciki, cillar da pillown da ya toshe kunnen sa yayi tare da durowa daga kan lafiyayyen gadon da yake kwance.Three quarter ne a jikin sa baƙi se Black singlet da suka karɓi tattausar fatar sa tare da sake bayyana hasken sa na farin mutum a fili, bedroom slippers ɗin sa ya zura tare da nufar ƙofa ya fita.Se yanzu na sami damar ƙare masa kallo, ƙaƙƙarfan namiji ne da kallo ɗaya za'a yi masa a shaida hakan saboda body building ɗin sa da ya bayyana ta cikin shimin jikin sa, taku yake irin na cikakkun maza masu isasshiyar lafiya da wadataccen ƙarfi har ya zagaya bayan ɗakin sa cikin son ganin wane mai tsautsayin ne ke masa ihu a ka bayan lokacin hutwar sa ne yanzu."Shegiyar yarinya mara imani, makashiyar banza makashiyar wofi se ɗan banzan kyau kamar aljana amma imani kam ko na ɗigon cokali babu a ranta, ba ke har kinsan ki kashe mutum ba, to muma se mun kashe ki da azaba a gidan nan, ku ƙara mata mana".Wata ma'aikaciyar gidan yarin ta faɗa aikuwa kattin matan suka kuma zage karfin su suka cigaba da jibgar ta kamar sun samu kayan wanki.Tsaye yayi yana kallon su da ɓacin ran da ya gaza boyuwa, wane irin iskanci ne wannan da za'a kawo masu laifi aiki baya dakin sa bayan ansan dole ne buƙaci hutawa, lallai dole ya nuna wa shugaban gidan nan ɓacin ran sa dan da alama kasancewar sa sabon fara aiki a nan yasa be San principles din sa ba.Mahaukaciyar ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play