ƘALUBALEN RAYUWAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

ƘALUBALEN RAYUWA

  • 1views
  • 4chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1 part 1

*ƘALUBALEN RAYUWA* Tsarawa/Rubutawa *SHAMSIYYA MANGA*__________________________ *Bissimillahir rahmani rahim* *Free page* *3&4* ___________________________Lokacin da Meenal ta ƙarasa cikin Kasuwar,yamma ta fara gabatowa a kwance ta tarar da mahaifiyarta tana bacci a gefen rumfar da suke kwana,ƙarasawa tayi wajen mahaifiyar tata wadda take ƙira da Ammah sannan ta fara tashin ta a hankali."Ammah ki tashi ga abinci na samo mana yau zakici abinci Allah yayi yau bazamu kwana da yunwa ba Ammah" aikuwa kamar an zaburi mahaifiyar tata haka ta miƙe cikin sauri tana rarumar hannun Meenal ɗin kamar mayunwacin zaki yaga nama, cikin sauri Meenal ɗin ta ciro gayan tuwon da ta nannaɗe a jikin hijab ɗin ta sannan ta ciro ɗankwalin kanta ta ajiye musu akai,ba tare da Ammah ta tsaya ɓata lokaci ba ta shiga rarumar wannan gayan tuwon tana cusawa a baki duk da cewa yana shaƙarta amma ko a jikinta,kafin kace mai har ta kusa cinye tuwon,hannu ta fara miƙa wa Meenal alamun tana buƙatar wani abu,cikin sauri Meenal ta sanya hannun ta tare da goge hawayen da ya zubomata wanda tun lokacin da Ammah ɗin ta fara cin abincin ta kafeta da ido sannan hawaye suka fara zubomata saboda tausayin mahaifiyar tata, duban Ammah ɗin tayi sannan tace"Ammah ruwa zaki sha" kai kawai Ammah ɗin ta iya ɗagamata sannan ta cigaba da tura gayan tuwon da yake gaban nata.Miƙewa Meenal ɗin sannan ta nufi wani waje a cikin kasuwar inda naga ana rubuta *GIDAN* *WANKA* ɓaro ɓaro a saman wajen,(irin gidajen wankan nan da ake samu a kasuwanni ko Tasha haka),wata leda Meenal ɗin ta samu sannan ta ƙarasa wani famfo da yake jikin gidan wanka ta tsuguna ta fara tarar ruwa a cikin ledar,Saida ta cikata sannan ta kama bakin ledar ta ɗore tare da nufar hanyar komawa wajen Ammah dan ta kaimata ruwan inda har a wannan lokacin idonta basu daina zubar da hawaye ba sakamakon tausayin halin da suka tsinci kansu da kuma irin rayuwar da suke yi ɗin a zuciyarta tana roƙon Allah da ya ci gaba da karesu.★★★★★Sanye ya fito cikin shirin shi na tafiya wajen aiki, matashine wanda a ƙalla bazai wuce shekaru talatin da biyar ba zuwa arba'in haka,dogo ne amma ba sosai ba yana da jiki dan har ɗan kamar tumbi gareshi amma kuma ƙibar ba wai irin sosai ɗinnan ba komai nashi dai daidai,tun daga ƙofar ɗakin shi ya fara cin karo da kwanuka wanda tun jiya suke a wajen, cigaba yayi da duban cikin falon inda yaga kaya duk a warwatse kamar an shekara ba'a gyara ba hakan shi ya tabbatar mishi da cewar hakimar bata tashi ba,dubanshi yakai izuwa kan dining inda yaga wayam ba komai,agogon hannunshi ya kalla yaga ƙarfe tara saura jijjiga kai yayi cikin tafasar zuciya sannan ya nufi hanyar ɗakin matar tashi,tura ƙofar yayi inda ya tarar da ita shame shame kwance a kan gado da alamu ko Sallar asubah ma batayi ba,ƙarasa shiga cikin ɗa...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “ƘALUBALEN RAYUWA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play