FreeArewaPen original
A CIKIN DUHU
- 1views
- 39chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Maryamkitty Dreams woven in words Kuna neman litattafai masu tsuma zuciya? Wanda zasu sanyaku tunani? Ku biyoni da alƙalamina domin samun nishadi da fadakantuwa
Sample · 01
A CIKIN DUHU…Kitty💕***@ Mssmeemah 01Kwanon gyad'ar da ta sayar ta kifa a kanta tana neman wurin fakewa saboda mamakon ruwan dake sauka. Da 'kyar ta samu rumfa 'kofar gidan wani mutumi da ta kasa gane wane gida ne saboda duhun da ya bayyana domin tanada tabbacin idan har ya fito ya sameta a wurin sai ya koreta. Tsanar da mutanen 'kauyennan ke musu ta rasa dalilinta, wannan labari ne da mahaifiyarta kawai zata iya bada shi.Jikinta gaba d'aya karkarwa yakeyi domin duk ta ji'ke gashi ruwan babu alamun zai tsaya nan kusa gashi gidansu da tazara. Hawaye ne ya biyo fuskarta wanda ya wanke a cikin ruwan yayin da ta tuna halin da mahaifiyarta da 'kaninta suke ciki a yanzu, idan anyi ruwa kad'an ma ya suke 'karewa balle mai yawa? Duk gidan nasu ruwa ya wanke 'kasar d'akin da suke kwana ne kawai ya rage shima Saida mahaifiyar tasu da kanta ta had'a 'kasa ta tottoshe wasu wuraren.Tana tsaye tana ri'ke da hannayenta har ruwan ya tsagaita yanda zata iya tafiya gida. Sauri take sosai cikin ruwan da ya kusa shanye rabin unguwar tasu domin ruwa ya kusa kaiwa gwiwarta amma bata damu ba, a wannan yanayin zata iya fad'awa rami ko rijiya amma sam ba wannan ne tunaninta ba, tunaninta kawai taje taga halin da mahaifiyarta da habu 'kaninta ke ciki.Tunda taga katangar 'kofar gidansu ta wanke taji gabanta na fad'uwa, da gudu ta fad'a tana Kiran "Baaba, Baaba!!"Turus tayi tareda mutuwar tsaye ganin mahaifiyarta dur'kushe bakin d'akinsu da ya ruguzo tana kuka tana kiran habu. Dur'kusawa tayi gefenta tace "Baaba me ya faru? Ina habu?""Karime katanga ta ruftawa habu, tun d'azu nake lalubensa da kiran sunansa Karime na kasa samo shi". A gigice karime ta zuba gwuiwoyinta a 'kasa ta fara ture 'kasar dake wurin, Banda karkarwa babu abinda jikinta keyi tana 'kwalawa habu kira saidai babu alamun habu ko muryarsa, can 'kasan wani gini ta hango yana motsi, nufar ginin tayi tana fad'in "habu, habu, kayi magana dan girman Allah" saidai hannunsa kawai ta hango yana motsi, muryar karime na rawa tace "Baaba mu nemi taimako a wurin ma'kwabta". " Karime bazasu sauraremu ba, nayi kuwwa nayi kuwwa amma babu wanda ya kawomin taimako". Karime tuni tayi jifa da mayafinta ta fice daga gidansu ta fad'a gidan dake gefensu wanda keda mata da yawa a ciki, da'ki d'aki take bi tana fad'in "Dan Allah ku taimaka mana gini ya fad'awa habu kar ya mutu, dan Allah ku taimaka mana". Babu wanda yayi yun'kurin taimaka mata hasali ma tamkar tana magana da iska haka wasu matan suka mata, kad'an daga ciki ne suke da 'karfin gwiwar jefa mata magana d'aya daga cikinsu tace "au shima zaku cinyeshi ne kaman yanda kuke cinye 'yan uwansa? Tir da hali irin naku Allah ya wadaran wannan zuri'ar taku, yanda shima ya mutu Allah ya kasheku duka mu huta". 'dayar kuwa turo 'kofarta tayi sannan ta ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.