FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Episode 1
*So ne*Page 1Labari da tsarawaMaman sharifa ce🔔📚*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*Bismillahirrahmanirraheem*Da sunan Allah mai rahama mai jink'ai,dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijimad'aukakin sarki da ya bani ikon kammala Nana khadijah kuma ya bani damana shiga sabon littafi na wato *SO NE* Allah ka bani ikon rubuta abinda zaiamfani al'uma, Allah ka tsare manaalk'aluman mu, Allah ka taimaki k'ungiyata abar alfaharina Jarumai writersassociation Allah kayi ruk'o dahannayen mu Amin. Ma daidai cin gida ne irin na wandayake da rufin asiri wanda ba za'asakashi cikin masu kud'i ba, kuma bayacikin talakawa,koda na shiga ciki manyan sora yene guda biyu irin ginin masu kud'in da, sai tsakar gida babba da d'akuna gudahud'u a ciki, d'aya na matar gidan,d'aya kuma na yaran ta mata,saikuma na yara maza na farkonshigowa gidan shine na maigidanwanda yake saukar bak'i idan yayi,kuma anan ne suke had'uwa dukansusuna karyawa da safe kuma suna cinabin cin dare ta re da Mai gidan,zan iya cewa gidane wanda aka ginashi ccikin tsantsar k'auna da girmama juna, yaran gidan sun sami ilimi da tarbiyyashiyasa na k'asa yana girmama na sama da shi,Abba shine sunan da yaran gidan sukekiran mai gidan da shi, zaune yake akanwata babbar dadduma, yayin da matarsa wadda suke cewa Umma take gefe tana zaune itama,Wata budurwa ce wadda zata kaikimanin shekara goma sha tara zuwaashirin zaune kanta ak'asa tanasauraron iyayen nata,Abba ne yayi gyaran murya sannanya ce""Muhasin cikin tattausan kalamiwanda ke nuna tsantsar nutsuwawadda ilimin addini kad'ai ke samarda ita,Inaso ki kula da kanki nasan kina dakamun kai kuma inada tabbacin bazaki bani kunya ba, ki sani university bakamar secondary bace wannan wajeneda kowa yake yin abinda ya zab'awarayuwarsa ba wanda zaice wani ya bari,ki sani ke ba kowaba ce kuma bay'ar kowa ba ce, wannan makarantarakwai 'ya'yan masu kud'i wad'anda bakaratu yake kawo su ba, saboda koda susunyi ko basuyi ba suna samungood results wanda kud'in iyayen suya ke siyamusu, fatana ko kumaince rok'ona a gareki karki biyewak'awaye kar kiga rayuwar wani taburge ki matuk'ar ba koyarwar addinin musulinci bace acikin rayuwar,sanan kimin alk'awarin rik'e mutun cinkidomin shine rayuwar ki, sannna uwa uba kiji tsoron Allah aduk inda kike, banyarda ki nema a wajanwani ba matuk'ar ina numfashi kodakuwa d'an uwa na ne , idan kikayi hakazanyi alfahari dake,yana kaiwa nan ya gyara zama ya kalliUmma yace ""idan kina da abinda za kifad'a mata kiyi sauri karta makara,Sauke numfashi Umma tayi ta kalli Abbata ce ""bani da abin fad'a komai ka fad'amata sai dai in k'ara jadda kalmarrike mutunci da kuma addini sannanaji tsoron Allah.D'ago kanta tayi ta kalli iyayen natatace naji duk abinda kuka ce kumain sha Allah zanyi k'ok'arin kiyayewa,bazakuyi kuka dani ba,albarka suka shiga sa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.