ƳAƳA MATA kyautar ubangijiFree

ArewaPen original

RandomFreeOngoing

ƳAƳA MATA kyautar ubangiji

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Alhamdulillah ala kulli halin

More from @fatimamusa

Sample · 16&17

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷         _*ƳAƳA MATA*_      _*(Kyautar Ubangiji)*_           _*BY*_     _*FAƊIMATU MUSA USMAN*_     _(Mnn khairi And Muslim)__*🥳SALLAMAR DASHEN🌲ALLAH*_*** LINK*_*** LINK*_*** ALLAH*_ _*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_  _*ALLAH SHINE GATAN MU*__{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️* لبسم الله الر حمن الر حيم_*Page*_ 16&17___________Da gudu ta ta je wajen da Baban na su yake tana sauke haki, kasa magana tayi sabida hakin da take sosai sabida gudun da tayi.  Yana ganin ta yayi saurin tashi daga zaunen da yake, su kuma jama'ar waje sun kasa magana sai binta su ke da kallo, kowannen su da kalar tunanin da yake yi a kan ta amma mafiya yawancin su tunanin wata babbar matsala ce tasa Zarah yin hakan da ta yi sabida sun san Zarah tana da nutsuwa duk da tana da rawan kan tsiya da shegen surutu, to amma sam bata da sakar ci, dan in tana tafiya kai ka rantse da Allah cewar bata son taka k'asa ne, dan haka wasu suke mata kirari da cewa *ZARAH BA KU'DI BA GADARA* duk da ita har ga Allah yanayin ta ne a haka, to sabida sanin halin ta shiyasa da yawa wasu suke zaton babbar matsala ce tasa Zarah yin wannan gudun.  Baban na su na tashi tsaye, ba tambayar ta ba'asi ba komai ya d'auke ta da wani gigitaccen mari wanda ya ratsa dukkan sassa na jikin ta.  Yana sauke mata marin ya rufe ta da masifa kamar zai ari baki "Mahaukaciyar ina ce ke Zara'u za ki cikin mutane da gudu haka?, ba nutsuwa ba komai, salon ki k'arasa zubar min da d'an guntun mutuncin da nake da shi a idon mutane ko?, to ahirrr d'in ki, daga ke har uwar taki kallon ku kawai nake duk kulla-k'ullar da kuke had'awa akan ido na kuke komai, shaaasha………".  Duk da Zarah taji shigar marin da mahaifin nata ya mata amma haka ta dake ta katse shi da cewa "Baba ka yi hak'uri dama zuwa nayi na fad'a maka Mama ta haihu".  Zarah na rufe baki Baban ya dafe k'irji gami da cewa " Shi kenan ta faru ta k'are, an kuma mace ta haifi mace, Allah sarki ni Malam Sani haka zan k'are rayuwa bani da magaji kullum da an tsuguna sai dai a haifo min jinsin da bazan ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play