pg 1Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

pg 1

  • 1views
  • 5chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writer

More from @oumayan68

Sample · BODARAR AMARYA

JAHAR SOKOTOYanayin yau Assabar mai daɗi ne tun safe an ta shi da sanyi, garin ya yi luf luf ba rana sosai ga wani iska da ake mai shiga jiki. Cike da ƙwarewa mai aikin ƙwalliya ke zizarawa Amarya ƙwalliya, duk da ana yi Amarya na faɗin albarkacin bakin ta, da kuma yadda ta ke son a tsara mata ƙwalliyar, hakan bai sa fuskarta da kyawon ta ya ƙara fita ba.Leshi ruwan ƙwai ta sa cikin wani ƙayataccen ɗinkin bubu wanda ya amshi jikin ta, mulamullan ɗuwawun ta sun bi rigar shar sun ƙwanta, kamar a buga su fara rawar itigi. Ɗauri me kyau akai mata da jinin karen ɗan ƙwali irin dai na amare, jika da takalma su ma jinin kare da mayafi ta yafa, ƙawar ta Surayya ita ta taimaka mata wurin saka mata sarƙa, da awarwaro da ƴan ƙunne.Tamkar yadda ake feshi haka mai aikin ƙwalliya ta feshe amarya da turaruka masu ƙwantaccen hankalin ƙamshi, daga nan su ka fito daga ɗakin da su ke zuwa farfajiyar gidan da ke cike tinjim da mutane, lungu da saƙo sai hada hada ake na buki, ga abinci da abubuwan sha birjit ana yawo da su.Ita ce a gaba ƙawayen ta sun ta ke mata baya, tafiya ta ke cike da salon ta na mulmula ɗuwawu gwanin sha'awa..."Ayiiiiririi ga Salamatu giwar mata, amaryar Hamisu ba da kan ki a sare, ahayyeh ba dai kyau ba kuma ƙira ba, duk ALLAH ya ba ki ga na bye ga na oyoyo" Washe baki Salamatu tayi a maimakon ta ƙara rufe fuskarta saboda alkunya, amma yane mayafin tayi tana kallon ƙanwar Inna da ke mata kirari, sauran jama'a sai barkallah su ke faɗin su na yaba kyawun Salamatu, wasu kuma sai 'ƴan ƙananun magangannu su ke tare da sadda kai su na ƙumshe dariya.SalamatuIn da su Inna su ke zaune da bataliyar maƙota da ƙawayenta har ma da abokan kasuwancin ta, ta nufa tana dariya, wata tafiya ta canja ci ke da salon da gwaninta kamar hawainiya ta riƙe ƙugu "Innata ga fa amaryar Hamisu guda ba ƙari ya kin ka ganni.""Tubarkallah Salamatu ɗiyar Inna, a gaskiya kinyi kyau yooo anya kuwa ke ce...? Kamar an sa ki injin an darzo ki." "Kamar dai in wanke goma in da fa ki."Rumgumeta Inna tayi cike da jin daɗi, mutanen da ke zaune wurin sai faɗin albarkacin bakin su su ke ga me da irin kyaun da Amarya ta yi.Daga nan in da aka tanada domin gudanar da walima,amarya da ƙawayen ta su ka nufa ba'a jima jama'a su ka fara taruwa ana hakan Mallama(Mai wa'azi) ta bayyana nan kowa ya gyara zama domin saurara, Malama ta fara wa'azin ta cike da ƙwarewa har ya fara ratsa zuciya da jikin mutane, ana tsaka da walimar...Salamatu ta ji wani ƙugi da uwar hanzanyarta ta buga,nan ta ke ta waro ido waje tare da cije gefen leɓenta, inda Inna da 'ywn uwanta ta duba damuwa a fuskarta, sai wani marairaicewa ta ke tana duban su tare da masu inkiya da ido, sai kash! Har yanzu ta kasa haɗa ido da su, tana cikin tunanin yadda zata yi hannunta dafe da ƙasan cikin ta, gefen daman ta ta duba sannan ta mai...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters5
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play