FreeArewaPen original
SALMAN MALEEK!
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Karamar marubuciya mai son faɗakar da Al'umma ta hanyar alƙalami, suna na Siddiqahtulkhaireey ni abokiyar karance-karance ce, a hakan ne har na fara rubuta littafi.
Sample · SALMAN MALEEK!
SALMAN MALEEK!Na shiga ban ɗauka ba...NaSiddiqahtulkhaireey Yahya(Matarso)GODIYADukkan yabo da godiya, su tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin sa su tabbata a bisa mu Annabi Muhammad (SAW).SADAUKARWAWannan labarin sukutum ɗin shi, sadaukarwa ne ga ƙawata, wato masoyita (dear) Ummi Sunisi, ki yi yadda kike so da shi, I really love u, Allah ya bar ƙauna.Shafi na ɗaya 01بسم الله الرحمن الرحيم"Jameel, ni fa zan faɗi gaskiya, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, game da abin da muka aikata, ina mai tabbatar maka alhakin shi bazai taɓa barin mu ba, gwara tun wuri mu faɗi gaskiya, kamar yadda wancen barrister ɗin ya yi mana alƙawarin, in har muka faɗi gaskiya za ayi mana sassauci"."Kai dallah malam gafara can, ai ban taɓa sanin daƙiƙi bane kai sai yau, mu faɗi gaskiya, ashe kai jaki ne kanka ba ya ja, to bari kaji duk wani waye-waye ƙarya yake, so suke su mana in giza mai kantu, kana faɗar gaskiya zaka rufta, in zaka iya bakinka ka iya, ka gane ai, ka daina banzan tunani." ya ƙare maganar yana bugun kafaɗar shi, kamin yabar gurin."ƙwal uba kaga wani kamar biri."A cewar Habu da sarkin gida ya turo shi yaga wa'inda sukai saura basu je wurin karɓar abinci ba."Kai tunanin me kake yi haka ka zabga uban ta gumi? Ko babarka ce ta mutu?."Ya yi maganar irin ta yaran nan gagararru.Ɗago da kanshi ya yi ya sauke su akan shi.Cikin maganar sa ta kangararru ya ce "Kai kamar ma kuka kake yi, naga hawaye kwance a Kuncinka, to kasan ba zaka iya ba uban wa ya aike ka kayi laifin da aka kawo ka, kai dallah malam ware, in zaka ware ka saki jikinka ka ware, uban wa ma kake wa kuka anan."Kafa yasa ya share shi ƙasa kana yabi takan ƙafafun ya wuce.tashi ya yi ya karkaɗe jikin sa, gami da ɗaukar robarsa, ya nufi gurin karɓar abinci.Tafe yake yana zuƙar sugari, yana fitar da yahaƙin ta hanci, ta baki, ji yayi an ce "kai zo ka bani sigarin nan."Oga Tajo da ya ji maganar, amma bai ga kowa ba, har zai wuce, sai kuma ya hange shi zaune bisa siminti, ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.Bayan ya matso kusa da shi, ya gama ƙare mishi kallo ya ce"kai ba ayi mana hauka anan, nan gidan ɗan kande ne, ba gidan ku ba.""I na san da haka, zaka bani ko sai dai ƙarfina ya bani?."Ya faɗa yana mishi kallon gargaɗi."Bazan baka ba, na ce bazan bada ba, kaga yaro, kai har ni za kayiwa barazana, ni zaka nunawa zafin kai, wa'inda suka fi ka ma naji dasu a gidan nan, ballantana..."Bai iya ƙarasa maganar ba, ta maƙale, a sakamon hannun sa daya kama ya banƙare shi baya.Ƙara oga Tajo ya saki, tare da magiya, akan bai san abin haka yake ba, don Allah ya yi haƙuri ya ƙyale shi, in dai sigari ce ya ɗauka, tsabar azaba, har da sakin fitsari ba tare da ya sani ba.Shiko Salman dariyar mugunta yake saki, yana nishaɗantuwa da ihun da Tajo ke yi."Kai! kai!."Wani gandiroba daya hango abin da ke faruwa ya tawo, ko da y...
App exclusive
Continue “SALMAN MALEEK!” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.