FreeArewaPen original
RAMUWAR GAYYA
- 1views
- 11chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1&2
⚫⚫ *RAMUWAR* *GAYYA* ⚫⚫( ~Tafi~ ~ta~ ~gayya~ ~zafi~ )_Labari/Rubutawa_*ZAINAB* *ABDULLAHI* *MUSA*( _Lailat_ _Abdullahi_ )---------------------------------------------------------*Tsokaci*Wannan labarin ƙirƙira ne ba dagaske bane,duk wanda yaji ko taji abinda bai yi masa ba acikin labarin to yayi haƙuri,domin ban yi shi domin wata ko wani ba.*Gargaɗi*Wannan littafin nawa ne haka kuma haƙƙin mallakar sa shima nawa ne,dan haka ban yarda wani ko wata yayi amfani da shi ta kowace fuska ba tare da amincewa ta ba,dan haka a kiyaye.----------------------------------------------------------*BISMILLAHIR* *RAHMANIR* *RAHIM*----------------------------------------------------------~Free~ ~Page~---------------------------*P1/2*Harabar kotun cike take maƙil da mutane babu masaka tsinke ko'ina ka duba iya duban ka mutane ne,duk wanda ka kalla fuskarsa babu alamun rahama ko sassauci ga kuma hayaniya dake tashi mai ƙarfin gaske kowa yana faɗar albarkacin bakinsa,idan bayan da jami'an tsaro dake ƙoƙarin dakatar da mutane tare da dukansu da kulakai da tuni sun afka cikin kotun sun yanke hukuncin da kansu ko sun huta da taraddadin da suke ciki.Duk da wannan ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi hakan bai hana wasu yin amfani da ƙarfin su tare da yin kukan kura suka bankaɗe wasu jami'an tsaro guda huɗu waɗanda suka zube ƙasa nan take,kafin kuma su miƙe su samu damar hana su tuni sun nufi ƙofar shiga kotun suna faɗin"ya zama dole alƙali ya yanke mashi hukuncin kisa,ko kuma mu mu ɗauki doka a hannunmu yanzu ya girbi abinda ya shuka",sai dai kafin su samu damar shiga kotun ne suka ji duka ta ko'ina babu ƙaƙƙautawa,jin da suka yi dukan yafi ƙarfin su yasa ba arziƙi suka koma baya cikin ƴan'uwansu ba tare da sun samu nasarar shiga cikin kotun ba,suka haɗe da sauran suka cigaba da jiran hukuncin da alƙalin zai yanke.*Cikin* *kotun*Acikin kotun shima cike yake da mutane sai dai saɓanin mutanen wajen,su na cikin a zaune suke babu mutum ko ɗaya da yake a tsaye,amma kamar yanda ake hayaniya a wajen kotun haka acikin kotun yin ta ake sai dai bata kai ta wajen ƙarfin sauti ba.Alƙali ne ya ɗago kansa tare da buga guduma ransa a matuƙar ɓace duba da wannan shine karo na ukku da ake samun hayaniya na tashi,gyaran murya yayi tare da cewa"duk wanda ya sake magana zai karɓi hukuncin kotu,"tsit kotun tayi tamkar babu mutum mai numfashi acikinsa kowa na tsoron hukuncin doka ta hau kansa,amma bawai dan haka suka so ba.Gyara farin gilas ɗin idon sa yayi tare da mayar da kansa akan wata farar takarda yayi ƴan rubuce-rubuce,sannan ya ɗago kansa ya fara magana"sakamakon ƙwararan hujjojin da suka bayyana na tabbacin wanda ake tuhuma ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi,dan haka wannan kotu ta yankewa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan kafin lokacin yanke hukuncin za'a ajiye shi a...
App exclusive
Continue “RAMUWAR GAYYA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.