FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
FATALWA BAƘAR TAFIYA SAKACI SALMA RAZANI WANI ƘARNI RUWA BIYU ƘULLALLIYA
Sample · 1&2
*AL'AMARINMU* *Na**MEENAT A ƳANDOMA**Labari ne wanda ban taba tabo irin wannan jigon ba, labari ne daya banbanta da sauran kada in cika ku da labari domin hausawa sun ce gani ya kori ji muje zuwa.**🌍MANAZARTA**WRITERS ASSOCIATION📚🖊*______________________________ *TSOKACI!**LITTAFINA NA KUƊI NE AKAN FARASHI 300 ZAKI RURO KATIN WAYA MTN KO KUMA KI TURO TA ACCOUNT AISHA ABUBAKAR 2151366600 U.B.A BANK, DAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA KADA KI TABONI🙏🏻**TALLAH*Albishirnku mata munzo maku da magani na gargajiya wanda zai saukarmaki da ni,ima yaqara maki lfy yawanke miki dattin mara daduk wani sanyi dake damunki,Ina amare dake shirin yin aure kafin kifara shan komai yakamata kifara da mgnn sanyi domin matuqar bakishaba kayan ni,ima bazasuyi tasiri ajikinkiba,Ina masu jego gadama tazo,Atafasa asa lipton da sugar da mada asha 2 times Muna katsina muna tura kaya ko ina yankatsina free deliver ne 1500 zaimiki 1month Ku tuntube mu akan wannan number *** 🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️@2023 January *PAGE 1️⃣&2️⃣*...Gagarumin hadarin da yayi ma garin ƙawanya ne ya haddasa ma garin matsanancin duhu wanda ko tafin hannunka baka iya gani, lokaci ɗaya iska ta fa ra kaɗawa da ƙarfin alamun ruwan sama yana gaf da saukowa."Manahil, Ridwana, Rizwana."Wata dajjijuwa dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun falon ta hau kwalama kira.A tare ƴan matan uku suka rusuna gabanta tare da amsawa."Kunci abincin dare"?.Dattijuwar da kallo ɗaya zaka yi mata ka fuskarci ƴan matan ƴa'ƴanta ne saboda tsananin kamar da suke yi."Aa bamu ci ba."Suka faɗa a tare."Maza ku bace mani da gani ku ɗauki abincin ku ku nufi dakin ku domin hadari na gaf da sakin ruwa maza sai Allah ya kai mu nima kwanciya zanje in yi."Tana ƙarasa maganar ta afka ɗakin tare da maido ƙyaure.Ƙaramar cikin su me suna Rizwana ce ta fara magana."Hmm! Umma kenan daga yau dai ba zaki kuma ganin mu a cikin gidan nan ba domin kuwa mun kusa bar maki gidan sai ki jiƙa ki sha."Ridwana ce tayi saurin bige mata baki."Ke fa baki da hankali, yanzu in Umma taji a tunaninki duk wani shiri namu bai wargaje ba.""Ki barta domin gaf muke da barin ta cikin gidan nan."Manahil ta faɗa.A tare suka shige ɗakin domin yanzu ba ta abinci suke ba hankalin su ya kaɗu akan su fara harhaɗa kayansu ko zasu aiwatar da abinda ke cikin zuciyarsu.Manahil ce ta ɗauki wayarta tayi kira."Ku kasance cikin shiri, gamu nan fitowa."Ƙit ta kashe wayar.Ruwan da suka ji an balle dashi ne ya basu damar haɗa kayansu cikin wani babban akwati, cikin sanɗa ba tare da sanin mahaifansu ba suka fice daga gidan zuciyar su cike da zallar farin ciki... ***...Mayrasa ne ya fa ra leƙa ɗakin mahaifan su cikin sanɗa domin tun safkowar ruwan saman ya ji su shuru, cike ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.