FreeArewaPen original
RUMBUN QAYA
- 1views
- 77chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample ยท TABA KA LASHE 1
DANDANO DAGA LITTAFIN ๐ฅRUMBUN QAYA๐ฅZAFAFA BIYAR 2023ยฉยฎHAFSAT Rano ***Tana tsaye gaban coat din sa dake rataye a jikin hanger da yake makaleta kullum yazo office din, waige-wage take tana son yin sauri ta dauki key din, sai da ta tabbatar da babu motsin kowa tayi saurin saka hannu a aljihun rigar ta jawo key din ta damke a hannun ta."What are you doing..." Ya fada yana tsaye daga bayan taSaura kiris glasses din idon ta ya fadi kasa, tayi saurin tare shi da dayan hannun ta juyo tana kallon sa. Takowa ya shiga yi har zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama har k'asa, kafin ya maida kallon sa zuwa wajen coat din tashi dake sakale."Me kike yi anan?" Yace muryar sa a d'an shake yana kallon fuskarta, kanta ta sunkuyar kasa sosai ya cigaba da kallon ta a nutse kafin yace"Are you trying to steal something?"Zaro idanun ta, tayi da sauri ta hau girgiza kai"Then tell me, me kike min a wajen rigana?""Am..am... Dama nazo na kawo maka wanchan report din da na hada ne, so sai na tarar kana restroom shine na ajiye a saman table shine sai naga kamar wani abu a saman rigar shine nazo zan duba na cire maka."Dan jim yayi yana kallon ta, kafin ya ja siririn tsaki ya nufi wajen zaman sa ya zauna."Show it to me."Yace yana jan mouse ya dora hannun sa akai. Fakar idon sa tayi ta tura key din a cikin aljihun jacket din dake jikin ta sannan ta karaso ta dauki report din ta bud'e ta fara masa bayani. Danne dannen sa yake har ta gama sai da yaji tayi shiru sannan ya dago ya dan kalle ta"Ina jinki." "That's all." Tace "Shikenan abinda kika iya samu?" Gid'a kanta tayi kad'an"Come here." Yace yana maida kansa ya cigaba da abinda yake, gefen sa ta matsa ta tsaya daga dan baya"Result din nake son gani, show it to me.""Ok!" Tace ta dan runkwafo kad'an ta shiga nuna masa. Kamshin turaren ta ne ya shige masa chan cikin hancin sa ya haifar masa da mixed feeling, dan muskuta jikin sa yayi yadda ba zata gane ba amma still yana jin kamar sake matso shi yayi."It's ok!" Yace da dan karfi"Just go, ki tura min ta email zan duba anjima.""Ok...Thank you" Tace dauki report din zata fita"Wait..." Yace ta juyo ta tsaya"Ki bawa Kamal shayi na ya kawo min.""Ok sir.""Sannan...karki kara saka turare me karfi idan zaki zo aiki.""Na'am?" "You heard me right! You may leave.""Ok." Tace da saurin ta, ta fice hadda dan gudun ta Tana fita ya saka hannu ya hau janye necktie din wuyan sa yana mikewa tsaye, ya isa gaban dan madaidacin fridge din sa ya dauki ruwa me sanyi ya hau sha"May I come in?" Ya turo kansa ya rike kofar ba tare da ya shigo ba"Kana da matsala, kayi ta tsaiwa a wajen." Yace yana dire robar ruwan ya shiga takawa zuwa seat din sa ya zauna. Shigowa yayi ya rufe kofar ya samu waje ya zauna shima yana murmushi "Ya akayi?" Yace yana duban sa "Akwai babban labari...""Ka...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.