FreeArewaPen original
ƳAR LEƘEN ASIRI
- 1views
- 3chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Alhamdulillah!🙏🤩💫🥀🦋
Sample · 1
ƳAR LEƘEN ASIRI Page 1-5 © Anup Janyau. *** @Mafel21. In Dedication To MaimunaAbdallah(CEO Heroine).❤️ *GARGAD’I!!!*_BAN AMINTA BA KUMA BAN LAMUNTA BA WANI/WATA SU JUYA/SANJAMIN LABARI TA KOWACE IRIN SIGA BA TARE DA IZINI NA BA. IDAN KUWA HAKAN YA FARU BAN YAFE BA_ Bismillahir Rahmanir Rahim. A hankali wani Yellow Helicopter ya fara saukowa a tsakiyar sunk'umin dajin mai fad'in gaske. Yana gama sauka k'ofar jirgin ta bud'u, ba b'ata lokaci mutanen da ke cikin jirgin suka fara fitowa da sauri-sauri har suka fice ga baki d'ayan su. Mutanen su biyar ne, Maza biyu Mata uku. Hud'un cikinsu riguna farare ne sanye a jikinsu, sai d'ayar macen dake sanye da red t-shirt, saidai matan sun d'ora wata leather jacket a saman rigunan jikinsu, kansu kuma sanye yake da sun hats, sai wasu black wellingtons boot dake sanye a k'afafuwansu. Ko wanensu akwai k'atuwar Backpack goye a bayan shi. Dukansu tsaye sukayi suna k'arema dajin kallo wanda yake kallo, don kuwa daji ne ba k'arami ba, saidai bayada wadatattun bishiyoyi a cikinshi, saisa duk inda ka d'ora idanuwanka iya ganinka. "Anya! dajin nan lafiya yake kuwa?". Cewar d'aya daga cikin mazan yana cigaba da wulga idanuwansa ta ko ina a cikin dajin. Gefenshi macen mai red t-shirt ta iso tare da fad'in, "Wallahi nima dai tambayar da nake yima kaina kenan tun d'azun, ko fa alamun gari babu a kusa"."Bamu shigo cikin dajin nan ba har saida aka tabbatar min da lafiyarsa, don haka karku wani d'aga hankullanku".Wata matashiyar budurwa kyakkyawa fara ta fad'a, tare da kallon wacce ke gefenta tana mai sake fad'in,"Hulaim! Ki yi amfani da na'urar hangen nesa ki dubo muna abunda ke yammancin mu, don can zamu dosa".Kai wacce ta kira da Hulaim d'in ta yi saurin gyad'awa tare da fad'in,"Okay! Ranki shi dad'e". Kana tayi hanzarin sauko da backpack d'in dake goye a bayanta, ta bud'e tare da ciro wata 'yar k'aramar na'urar hangen nesa, sannan ta d'an yi gaba tare da saita na'urar a yamma ta d'an leka idonta d'aya ta fara hango musu. Tsawon wasu mintuna ta juyo tana kallonsu tace; "Ranki shi dad'e!, akwai gari a gaba, saidai kafin mu isa garin zamuyi kusan tafiyar awa d'aya".Wani irin zaro idanuwa waje mai red t-shirt tayi tare da fad'in, "Awa d'aya fa kika ce?, haba! fisabilillahi taya zamu iya tafiyar awa d'aya a cikin wannan daji?". D'an murmusawa kawai Hulaim d'in tayi ba tare da tace mata komai ba, ta mayar da ...
App exclusive
Continue “ƳAR LEƘEN ASIRI” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.