FreeArewaPen original
Wani Gari
- 1views
- 86chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Official Khadeeja Candy ✍🏻 Author • Entrepreneur CEO, Khadeeja Candy Store ☎️ •- ***
Sample · 01
Baya baya ta yi ta lankwasa kamar za ta fadi sai kuma ta yi gaba tare da cira kafarta ta dama sama kafar da ta sha ado da fararen yayan wuri ta buga a kasa cikin tabon lakar ruwan saman dake sauka, ta mika hannayenta duka biyu sama ta ware karan dake hannayenta ta buga su da karfi har sai da suka yi kara, sannan ta fara juya k'ugunta yayan wurin dake daure a kwankwasonta suka fara kara, a take maza da matan dake gurin suka hau tafi, masu ganguna irin na itace suna dukawa sai ta rufe ido tana taka rawar da ta zame musu ta al'adar wanda aka saba gabatarwa sau daya a kowace shekara. Wata siririyar busar sarewar ce ta rika tashi a tsakanin mazanjen da ke buga gangunan kidan, a take kowa ya fara rausayar da kai domin busa ce dake saukar da natsuwa da annashuwa tare da nishadin zuciyar duk wani mai saurarenta, ciki kuwa har da Sarkin Garin Garuk da yan majalisun masarautarsa da kuma fadaw...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.