FreeArewaPen original
DAUƊAR GORA....!!
- 1views
- 145chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
1.........Kwanakin mako uku kenan da shuɗewar komai amma komai ya kasa mantuwa a zukatansu. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jiki. Duniya ta masu ƙunci, ƙunci irin wanda har ƙarshen numfashi da wahala su manta. Farin cikinsu ya zama fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na ƙasa da su. Da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai. Kafin shuɗewar makwanni uku masu ɗauke da kundun baƙin ciki rayuwar ahalin Mal. Zayyan tamkar dutsen lu'u-lu'u suke a cikin tsakkiyar zinare. Ba magana ake akan dukiya ba, dan tana a cikin jerin abu mafi rauni da suke ɗauka ko amsa sunan ko kallo farin ciki. ana magana ne akan kammaluwar ahali masu matuƙar ƙaunar juna zunzurutu mara gauraye. Masu kuka a yayin zubar hawayen ɗayansu, ...
App exclusive
Continue “DAUƊAR GORA....!!” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.