FreeArewaPen original
GWAGWARMAYAR ƘAUNA
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Shafi na 1
💞💞💞💞💞💞💞GWAGWARMAYAR... ƘAUNA💞💞💞💞💞💞💞Mallakar...KHADIJA SALIS IBRAHIM(Maman Amatullah)SARAUNIYAR JARUMAI👸JARUMAI WRITERS ASSOCIATION📚💪🏻YABO..Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah Mai Kowa Mai Komai, tsira da aminci su ƙaru ga Annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. GARGAƊI...Ƙirƙirarren labari ne ban yarda a juya min shi ta kowacce siga ba, ba tare da izinina ba. A kiyaye! Wannan littafin na ƙuɗi ne N300 ki biya kafin ki karanta.*ABBA ABUBAKAR YAKUBU* wannan littafin daga farko har ƙarshensa sadaukarwa ne a gareka. Ina godiya da kulawa, Allah Ya saka da Alkairi. Haƙiƙa kai ɗin na musamman ne. Allah Ya ƙara girma da ɗaukaka, Ya cika rayuwarka da ta iyalanka da farin ciki, Jarumin Jarumai!!! 😍Shafi na 1️⃣ Free page Gudu suke shararawa na fitar hankali, kamar za su tashi sama, in ka ga yadda suke gudun abin zai baka tsoro, domin za ka ɗauka wani ne ya biyo su, ko kuma ka yi zaton wasan tsere suke yi. Haka motar ta kutso cikin dajin ba tare da sun lura da dabbobin da ke faman kaiwa da komowa suna yin kiwo ba. Ko da motar ta zo wani rami mai cike da ruwan caɓi ji ka ke facal, ta faɗa tare da fallatsa dukkan wani abu da ke kusa da ita. Wani wawan burki motar ta ja ji ka ke ƙuuuuuuu! Hakan ya faru ne sakamakon hangen wata matashiyar budurwa da ke tsaye a gaban motar, hannunta riƙe da sanda. Tana sanye da kaya irin na fulani, sai dai gaba ɗaya sun ɓaci da caɓi, alamu sun nuna ta fito kiwo ne. Cikin zafin nama da ɓacin rai mamallakin motar ya fito a fusace fuskarshi cike da ɓacin rai. Ya ɗaga murya yana mata tsawa, "Ke, wacce irin daƙiƙiyar yarinya ce ba kya gani! An faɗa miki nan ɗakinki ne, ko kuma gurin wasan ki ne? Ba ki san idan na take ki na take banza ba. Ko kina tunanin in na take ki na wuce wani abu zai faru ne to, kin yi kuskure. Idan na doke ki na doke banza, don babu abin da za a yi. Da take ki da take kaza duk ɗaya ne a wajena!! Ƴar ƙauye da ke matsa min a hanya ko na yi ciki da ke sakaryar yarinya!" Ko gezau bata yi ba, balle ya sa ran za ta matsa ta basu guri, sai ma ƙara gyara tsayuwar sandarta da tayi. A cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsa, a hausar da bata isheta ba ta fara faɗin, "Kai wanne irin sakarai ne wanda bai san darajar mutum ba, balle dabbobi? Ko an faɗa maka nan ɗin kai ɗakinka ne da za ka yi yadda ka ke so to, ka yi kuskure! Nan hanya ce, kowa na da haƙƙi da ita ba ikon ka ba ce. Don haka ka dawo cikin hankalinka, ba na son sakarci. Kai da ganinka tarbiyya ba ta wadace ka ba, sakarai wanda bai san darajar ɗan A..." Ji ka ke tas! Ya ɗauke ta da wani lafiyayyen mari wanda ya yi sanadin rufewar bakinta ba tare da ta shiryawa hakan ba."Ke! Ki iya bakin ki ki san irin maganganun da za...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.