KARYA DA GASKIYA                                                       cigaban  TAFARKIN TSIRAFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

KARYA DA GASKIYA cigaban TAFARKIN TSIRA

Author
Author
  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Karya da Gaskiya BABI NA FARKO

KARYA DA GASKIYA Cigaban TAFARKIN TSIRARubuta LabariMANSUR USMAN SUFISarkin Marubutan YaƙiBABI NA ƊAYA   Al'amarin da firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kenan suka sha jinin jikinsu, a lokaci guda Fitinatul-Amir ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, kawa sai ya dubi waɗansu ZARATAN DAKARU dake tsaye a gefen shi cikin matuƙar fushi ya buɗi baki ya ce "Ya ku dakaru ina so ku yi hanzari ku bi sahun dakarun dake ɗauke da haraji ku tabbatar da cewa ba a sanya dukiyar sarki Madsur a cikin Baitul-Mali ba, kuma ku tabbatar da cewa kun kawo mini Madsur da tawagarshi cikin ƙoshin lafiya domin na yanke masu hukunci dai-dai da abin da suka aikata mani,Na rantse da girman halarar tsafi na idan ku ka yi kuskure a wannan aiki da na baku sai KAIFIN TAKOBI ya sha jininku...,Kafin sadauki Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi dakarun su kimanin dubu sun zare makamansu sun ruga izuwa wajen fadar suka bazama cikin gari wasu bisa dawakai wasu a ƙasa, domin farautar sarki Madsur.   A she a ɗazu lokacin da Fitinatul-Amir ke tattaunawa da yaro Usaiba, kuma abin da Usaiban ya faɗa ya tabbata bayan Fitinatul-Amir ya gudanar da bincike 'yan majalisa sun ji da kunnuwansu, nan take suka raya a cikin cewa haƙiƙa wannan yaro yakasance ɗan baiwa taban mamaki, wai shin ma mene ne alaƙar dake tsakanin su, Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, kawai sai suka zuba idanu domin su ga sakamakon da dakaru za su dawo da shi.     Al'amarin sarki Madsur da tawagarshi kuwa, lokacin da suka fice daga fadar Fitinatul-Amir, sai Madsur ya karanta ɗalasiman tsafi suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, ba su bayyana a ko ina ba sai a fadar Madsur dake cikin babban birnin Hairul-Maswat, Fadar yakasance makekiya da aka ƙarara da nau'ikan ababen more jin daɗin rayuwar duniya, a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a makaɗa, mawaƙa tare da dukkan wani mai faɗa a ji, lokacin da sarki ya zauna bisa kan karagar mulki sai waɗansu irin tsala-tsalan 'yan mata kuyangi suka shigo fadar ɗauke da nau'ikan kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe suka shiga raba wa jama'a, nan al'umma suka fara kimtsa cikinsu cikin nishaɗi da annashiwa, makiɗa da makawa suka fara aikinsu na raye-raye da kiɗe-kiɗe domin ƙara wa al'umma nishaɗi, shi kan shi sarki Madsur tashi ya yi daga kan karagar mulki ya cire alƙyabbarshi ya zauna cikin 'yan majalissa suka shiga yin walimar suna shewa da tafi, da yawa daga cikin al'ummar dake fadar ba su dalilin da ya sanya aka shirya wannan walima ba, domin tsawon shekaru sarki Madsur yana buƙata daga sharrin Fitinatul-Amir amma bai taɓa farin ciki tamkar yau ba, ana tsaka da wannan walima ne sarki Madsur ya karɓi wani kofi mai ɗauke da barasa a hannun wani hadimin shi ya kai bakinshi da nufin...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “KARYA DA GASKIYA cigaban TAFARKIN TSIRA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play