FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
🌍🌍🌍⚜️⚜️⚜️🌍🌍🌍 *BURI UKU*🌍🌍🌍⚜️⚜️⚜️🌍🌍🌍 _*Mallakar*_ *Rasheedat Usman* _(Ummu Nasmah)_*بسم الله الر حمن الر حيم*___________________________________*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼**🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```*** shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻*** Book*Godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani ikon samun damar rubuta wannan labarin, tsira da aminci su tabbata ga cika makin Annabawa Muhammad (SAW) har izuwa iyalan gidansa da Sahabbansa, Allah ya bani ikon rubuta dai-dai abinda zamu amfani gaba ɗaya.SADAUKARWA *Ga Ahalina GIDAN SHANU DUTSE ina matuƙar alfahari gareku.*GODIYA TA MUSAMMAN *Ga Kakana farin cikina Alhaji Babba, gidan shanu Allah ya jiƙansa da rahama ya yafe masa kurakuransa yasa mutuwa ta kasance hutu a garesa.* _*MARUBUCIYAR*_-Nasmah Ko Nasirah.-Sauyin Rayuwa.-Sara Da Sassaqa.-Akan Ƴar Uwata.-Indo A Birni.-So Bai San Jini Ba.-Hatsabibiya Saude.-Ruɗanin Zuciya Biyu.-Doctor Hassan.-Ƙauyen Mu-Gelle Bingel.-Aminaina Ko Ita?-Ƙullalliya.-Jalala. *Tsokaci*Ƙagaggen Labari ne banyi sa dan cin mutuncin kowa ba, idan kinga/kaga yazo dai-dai da yanayin rayuwarka ko halinki labari ne yazo da haka. *Gargaɗi*A guji juya min littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba ƴan You Tube a kiyaye, yin hakan kuskure ne kuma zan iya ɗaukar mummunan mataki. Gareku ɓarayin fasaha wadanda bakwa ramin kanku sai wani yasha wahalar haƙar nasa ku afka, to ku fita daga idona na rufe duk shegiyar yarinyar da ta kuma shiga gonata, tabbas sai na yi fatale da ita, a kiyaye kowa ya iya allonsa ya wanke IDAN KUNNE YAJI........*Page 1*"Lubna ita fa Nakasa ba Kasawa bane! Meye aibun Ahmad dan yace yana sonki ko na kasarsa itace Aibun nasa, ko shi ya halicci kansa? Saboda yace yana sonki shine zaki wulaƙanta sa? Kifa ji tsoron Allah Lubna banga laifin sa ba dan yace yana............." Wani irin matsiyacin kallo Lubna ta jefawa Samra bakinta ta taɓe tare da zubar da miyau cikin ƙyama da jin ƙunar maganar Samra Lubna tace. "Ya isa haka Samra kunnena ya fara gajiya da jin waɗannan baƙaƙen kalaman naki marassa daɗin sauraro!! Allah ya tsari gatari Noma!! Dubeni da kyau sama da ƙasa Samra kinsan ko da girgije kurna t...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.