FreeArewaPen original
BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?)
- 1views
- 5chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
writer
Sample · Mafari.
*PAID BOOK 300**BIBIYATA YAKEYI*_(WAYE SHI?)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ZAYNAB BAWAMarubuciyar *BIBIYATA AKEYI**Y'AR FARI**YARIMA FAYAD* paid 200*ƘADDARAR RAYUWA**Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA! TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI). WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI! BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝*Allah yabani ikon rubuta muku abu mai amfani kamar yanda nafarashi Lafiya Allah yasa nagamashi lafiya.*Page 1Jin alamun za'a shigo ɗakin ya sanya nayi saurin ɗauke idanuwana daga kan madaidaiciyar tv ɗin dake manne ajikin bango nayi saurin maida hankalina ga littafin dake gabana. Da sallama ta buɗe labulan ɗakin ta shigo ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin falon. Matashiyar matace wacce bazata wuce shekara talatin da takwas ba. Kallona tai ta taɓe baki ta zare remote tana faɗin. "Nida ɗakina amma ban isa abarmin tashar dana keson kalla ba kulllum sai dai wannan tashar kwallon ta jaraba, ke kina mace ni bansan mai ya hadaki da wannan kallan kwallon azabar ba." Nidai bance komai ba harta canja tashar ta maida zuwa tashar shirye-shiryen Hausa sannan ta ajiye remote din. Mikewa nayi ina zumburo baki nafice daga ɗakin ina jiyota tana faɗin. "Dama nasani wannan karatun na munafunci ne kallon ball kawai kike yi." Nidai bance komai ba na wuce zuwa ɗakin matar mahaifina wacce muke kira da Aunty na zauna na cigaba da kallon ball ɗina acan. Sai da aka gama sannan raina yayi sanyi domin tawagar da nake so itace ta lashe wasan kwallon. Raina fess na fito na nufi ɗakin mahaifiyata. A uwar daki na sameta na shiga na zauna tana faɗin. "Angama kallon ball din kenan?" Batareda ta jira amsata ba ta cigaba da fadin. "To sai amaida hankali maza ayi karatu tunda angama ibadar." Zumburo bakina nayi nace. "Nifa dama Mama na rigada nagama karatu, kawai bita nake yi." "Gara dai ki maida hankali kiyiwa kanki faɗa Mamee kitsaya kiyi wannan karatu dakyau ke kanki shaida ce kinga yanda aka samu kika fara wannan karatu, har indai kikaki nutsuwa kici wannan jarabawar kika fadi kinsan yanda mahaifinku zai ji. Idan kuma so kike ki karasashi toh, kina gani dai da ya ya aka yi aka hado har dubu casa'in aka biya miki rijista dan kawai kin nuna kina so, idan kika zuba masa kasa a ido baki yiwa kanki adalci ba. Ki daure kiyi karatu kici weeding ɗin nan in sha Allahu har indai kin wuce zamu san yanda zamuyi mu hada karfi da karfe wajan ganin mun taimaka kinci gaba. Id...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.