SARAN ƁOYE!!Free

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

SARAN ƁOYE!!

  • 1views
  • 20chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1

..........Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin.    Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma.    Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.   Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama'ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.    Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.     Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama'a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za'a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.     Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa.      “Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o'e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”. Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙya...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters20
premium19
02

2

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
03

3

Premium
Updated 10 months agoAvailable now
04

4

Premium
Updated 10 months agoAvailable now
05

5

Premium
Updated a year agoAvailable now
06

6

Premium
Updated a year agoAvailable now
07

7

Premium
Updated a year agoAvailable now
08

8

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
09

9

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
10

10

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
11

11

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
12

12

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
13

13

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
14

14

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
15

15

Premium
Updated a month agoAvailable now
16

16

Premium
Updated a month agoAvailable now
17

17

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
18

18

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
19

19

Premium
Updated a month agoAvailable now
20

20

Premium
Updated 9 days agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play