FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writer Aysha A. Bagudo
Sample · MUWADDAT : PAGE 1
💗💗💗💗💗💗 MUWADDAT 💖💖💖💖💗💗💗💗💗💗 ~NA~ *AYSHA A BAGUDO*Page 1 ~DEDICATED TO~ _AUNTY SALAMATU AYYUBA_ _(UMMIN KADUNA )__karamacinki da alkharinki tattare da mutuncinki gareni, ba zai misaltu ba, aunty ummi nah , ina sonki irin soyayyar da 'yan'uwantaka kad'ai ke haifar da hakan , ina rokon Allah ya barmu taren tare har karshen rayuwarmu, Allah ya k'ara damkon kauna da zumunci atsakaninmu, love you so much my special aunty ,kaf media babu aunty tamkar ki ,shi yasa zan sadaukar da gabadaya novel dina gareki domin kin cancaci fiyye da hk a zuciyar bagudo_alhamdullahi am back again.warning!!! for the first time !!!! i will like to say," don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people ,if you read it is for your own risk .....*** @HAUESHbismillahirrahmanirrahim ....Ayshatul muwaddat kwance take akan lafiyayyen gadonta kiran italy, amman ba bacci take yi ba, kurun dai ta kwanta ne tana tunanin Muhammad auwal ne bisa tsarin zuciyarta. cigaba tayi da tunane tunanen zucin data Saba, Wanda ya rigada ya zame mata jikinta ,a duk sanda ta ke'be kanta to fa Bata da wani aiki sai na tunaninsa, yayinda zuciyarta zata yita kissama mata yadda sufofinsa jikinsa suke had'e da yanayin tsarin rayuwarsa ,komai nashi Yana matukar burgeta most especial sautin muryarsa Mai shiga jiki da tsayawa arai ,da tsarin halittarsa , naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske had'i da lalibo wayarta dake ajiye a saman bedside tashiga neman layinsa .Kira daya biyu ya d'auka cikin sanyayyiyar muryarsa "hello Aysha nah .. .... Tana jin sautin sanyayyiyar muryarsa mai shiga jiki ta lumshe idanunta, tana fesar da numfashi saboda wani Abu da taji ya tsarga mata tun daga cikin kwakwaluwar kanta har zuwa kasanta ya dinga yawo a koina a sansar jikinta.Shiru sukayi gabadaya batare da kowanensu yayi yunkurin furta wani Abu ga d'an'uwansa ba ,illa numfashi da ajiyar zuciyar da suka dinga saukewa a tare Yana ratsa kowani Shashi na gangar jikinsu .Jin tayi shiru taki magana yasa yayi karfin halin fixgo magana yace "Aysha nah kin kirani sannan Kuma kin yi shiru , gashi zuciyata na sanar min da cewar akwai abinda bakinki yake son fad'i shiyasa Kika kirani ,me ke damunki ?"ki sanar min da damuwarki kinji ....Tayi shiru tsabar miskilanci dake *** ,duk da dai maganar take son yi Amman harshenta yaki sarrafuwa Gurin lankwasa shi ,har sai daya sake yin magana "ki sanar min da damuwarki Aysha nah , domin sanin haka shi zai sa na samu natsuwar zuciya, akasin haka Kuma kin san tashi hankali ne gareni , Dan haka kiyi hakuri ki sanar min kinji ta hannun damana.Jin yadda ya wani marairaice mata yasa ta bud'e bakinta da kyar tace "babu komai fa kawai dai na Kira ne mu gais...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.