LAUJE A CIKIN NAƊIFree

ArewaPen original

MysteryFreeCompleted

LAUJE A CIKIN NAƊI

  • 1views
  • 9chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

Marubucin littattafa, waƙoƙi da fina-finan Hausa ɗan asalin jahar Bauchi mazaunin ƙaramar hukumar Darazo. Please, follow me. ***

More from @elder

Sample · 01

Bismillahi Rahmani Rahim!Budurwar tana zaune cikin tsananin damuwa, ta kifa goshinta a kan hannayenta da ta naɗe su ta ɗora a kan gwiwowin ƙafafuwanta da ta takure su waje guda.Dije, sanye take da atamfar zaman gida; riga da zani da kallabi, bayan haka babu komai a jikinta hatta ɗankunne ko kuma zobe da makamanta. Ta jingina bayanta da bangon ƙuntacaccen ɗakin da ɗan sararin cikinsa yake wayam, a Hedikwatar 'yan’sanda ta jihar Bauchi, da ke a babban birnin na Bauchin Yakubu.***Babban ofishi ne, mai ƙunshe da komai da komai da ya cika bunƙasarsa, na Mataimakin Shugaban Rundunar Hukumar 'Yan’sandan Jihar Bauchi (DCP), da ke cikin Hedikwatar.Da babban teburi a gaban kujera mai juyi da take ɗauke da natsattsen Dcp ɗin, a daidai lokacin na yammaci.Sanye yake da inifan ɗin aikinsa mai ɗauke da tamburan da suke zayyana girman matsayinsa. Hularsa tana gabansa yana ɗan jujjuyawa cikin isa da waya maƙale a kunnensa a riƙe, yayin da hasken lantarki ya zama tarwal, wata tsayayyiyar na’urar sanyaya muhalli da take can dungu sanyinta yana ratsa komai da ko'ina, da na’ura mai ƙwaƙwalwa da takardu da wasu tarkacen amfani. Sai wayar talfo da wayar tafi-da-gidanka, gefe guda ƙaramar tutar Najeriya ne kafe duk a kan faffaɗan teburin.Akwai manyan-manyan hotuna manne a jikin bangon ofishin. Na Shugaban Ƙasa; Gwamna; Sarki; Kwamishinan 'Yan’sanda da na shi kansa Mataimakin.“Ni ne fa na faɗa maka ka kwantar da hankalinka, Alhaji. Duk wanda yake da sa hannu a ta’asar da aka yi maka zai shigo hannunmu ba da jimawa ba. Eh…” Ya saurara kaɗan kana ya ɗora. “…Ka ba ni gajeren lokaci kawai, za ka ji duk abin da yake akwai… To... To shikenan… Kar ka ji komai. Bar komai a hannuna…. Na gode ni ma".Ya sauƙe wayar ya ajiye, ya ɗauki wani fayil a gabansa ya bankaɗa ya fara dubawa a sannu.Lokacin aka turu ƙofa. Ya ɗago kai yayin da idanuwansa suka kai kan Inspector Nasir: Matashin ɗan’sanda, wankan tarwaɗa, mai faffaɗar fuska da ɗan tashasshen hanci da cin zuma a haƙoransa biyu na gaba. Yana da matsakaicin jiki da tsayi, ga kuma kyakkywar ƙira.Ya iso gaban Mai girman sanye da kakin aiki ba hula. Ya tsaya ya sandare, ya miƙe hannayensa a jikin cinyoyinsa ya dunƙule tafukansu tare da haɗe tsakanin ƙafafunsa. Cikin risinawa ya ce “Sir!”Dcp, ya amshi gaisuwar yana mai miƙa hannayensa gaba tare da dunƙule tafukansu, ya sauƙe yana mai duban Inspector da faɗin, “Ya aka yi, Inspector?”Cikin girmamawa ya yi Magana. “Sir! Yarinyar nan fa mun yi iya yinmu ba ta ba mu wani bayani ba... Sam!”Dcp ya yi shiru kaɗan yana kallon sa cikin nazari kana ya ce, “Mu je na gan ta…” Ya tashi, ya fita daga makewayin da mazaunin nasa yake, ya wuce gaba, Inspector Nasir ya bi shi a baya suka fice...***Dije, ta ɗago da kyakkyawar fuskarta marashin annuri tsawon lokaci, wadda hawaye ya yi jurwaye a kanta, ta dubi mu...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “LAUJE A CIKIN NAƊI” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play