FreeArewaPen original
NA SAKE TA!
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Author
Sample · 1 Complete
NA SAKE TA!Asabar 7:30 pmYanzu da nake zaune a ɗaya daga cikin kujerun alfarmar da suka yiwa katafaren falon saukar baƙin matashin ɗan kasuwa Usman One Boy ƙawanya ina raba idanun ta inda zan ga ɓullowarsa ƙarfe bakwai da rabi 7:30 dai-dai tafkeken agogon bangon da ke saƙale a jikin bangon yamma na falon ya nuna.A hankali na kai duba na ga farantai guda biyu da ke gabana kan madaidaicin teburin gilashi, ɗaya shaƙe yake da kayan marmari, ɗayan kuwa soyayyen naman kaza ne, sai manyan kwalayen Juice har guda uku da kofunan glass. A ƙalla mintuna na biyu a zaune kuma tun shigowa ta ɗaya daga cikin hadiman gidan ya gabatar min da waɗannan kayan maqulashe bisa umarnin uban gidansa.Na sauke ajiyar Zuciya a hankali tare da ɗauke kaina zuwa hanyar ƙafar bene lokaci guda da ƙamshin turaren Usman One Boy ya haɗe ko ina a falon, ya bayyana cikin shigar alfarma irin ta matasan attajiran da naira ke zigawa a lokacin su, ya tako har inda nake zaune ya bani hannu muka gaisa, kana ya samu guri shima ya zauna kujerar dake nesa da ni kaɗan yana kallo na."Kamal baka taɓa komai ba da aka kawo maka, ka saki jikinka fa." Ya faɗa yana gyara zama.Kaina a sunkuye na miƙa hannu na ɗauki kwalin lemo guda ɗaya na farke na tsiyaya a kofi, na fara kurɓa a hankali."Ashe ka samu saƙon kirana?" Ya tambaya."Eh, tun jiya ma, kasancewar babu mota a hannuna yasa ban samu ɓullowa ba sai yau." Na amsa masa."Allah Sarki! To ya aikin naka?""Alhamdulillah! Muna nan muna lallaɓawa." Na sake amsawa a karo na biyu.A baya Usman ya yi min farin sani kasancewar duk tare muka taso a unguwa ɗaya tun ƙuruciya, bisa la'akari da yadda ya ke kama sunana kai tsaye yanzun ma bai manta ni ba duk da sauyin rayuwar da ya samu."Na kira ka nan ne domin ƙaruwa Kamal, da fatan ba za ka yiwa magana ta mummunar fahimta ba." Ya faɗa bayan ya sauke ajiyar Zuciya."Babu damuwa Usman kai nake saurare."Ya numfasa a hankali, "Kamal wata buƙata ce da ni, ta wata fuskar kuma za mu iya kiran ta kasuwanci tsakanin ni da kai bisa yarda da amincewarka." Ya saurara kaɗan tamkar yana jin nauyin furta abinda yake son faɗa sai kuma ya ci gaba bayan ya yi ƙasa da muryarsa."Babu batun ɓoye-ɓoye, bari in yi maka gwari-gwari Kamal, so nake ka saki matarka Hajir, zan baka Naira miliyan biyar, ina so zan aure ta."Lemon da na kurɓa ya dawo sakamakon sarƙewar maƙogwarona sannan kofin dake hannuna ya suɓuce ya faɗi kan rigata duk ta ɓaci da ruwan lemo.***Litinin 8:00 pmNa runtse idanuna na buɗe a hankali, burina in shafe ire-iren kalaman Usman daga kwanyata, duk a ƙoƙarina na zama jarumi wajen yiwa Hajir halaccin da zai ci gaba da kafa kyakkyawan tarihi a soyayyar da muka shafe sama da shekaru huɗu kafin ta kai mu ga aure, amma abin ya faskara, alal haƙiƙa na san hakan baya rasa nasaba da baƙin talaucin da ke bibiyar rayuwata kamar inuwa, i...
App exclusive
Continue “NA SAKE TA!” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.