HUBBAN SHADIDAN 1Free

ArewaPen original

RomanceFreeCompleted

HUBBAN SHADIDAN 1

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · Book 1

HUBBAN SHADIDANKwana da wuni ana faman tafka ruwan sama, haka ne ya haddasa wa qauyen ya xauki sanyi yayin da sahu ya xauke, duk kuwa da cewar yammaci ne. daidai wannan lokacin Hadiza tare da maigidanta Iro sai xiyarsu Ainau zaune a gefensu, tana karanta musu littafin tatsuniyoyi. Iyayen nata na sauraronta cike da jin daxi da shaawa, a daidai lokacin da tatsuniyoyin suka xau daxi, a lokacin ne tunkiyar da suka yi ma tirke a soron gidan ta hana wa kunnensu saqat da kukanta. Iro ya dubi Hadiza.Wai shin kin bai wa wannan tunkiyar harawa kuwa?Bai shigo xaka ba sai da na juye mata na cikin buhun nan, yanzu haka zai kai mata har safe.Ainau ce ke qoqarin yunqurawa.Abbana bari in je na duba. Aa yi zamanki, bara in duba. Hadiza ta faxa lokacin da ta ke qoqarin yunqurawa, hakan ne ya sa Ainau ta koma.Lokacin da ta qaraso harabar gidan kukan tunkiyar yaa tsananta, a sukwane ta isa gurin. Abin da ta yi arba da shi ya sanya numfashinta ya yi xaukewar wucin gadi, lokaci guda ta qwalla ihu, Iro da ke can xaki bai san saadda ya bazamo ba.Yau mun shiga uku, qarshen duniya da ake hwaxi mana shi ne ya zo? Ya ce a daidai lokacin da ya yi arba da Isuhu tsirara haihuwar uwarsa ya haiqe wa tunkiyarsu.Da ganin haka Isuhu ya yi saurin rabuwa da jikin tunkiyar ya shiga zaro ido tare da kicin-kicin sanya wandonshi, kan kace kwabo wuf! Ya yi waje yana faman muzurai.Hadiza na faman tafa hannu cikin tsananin firgici, Ni ya su, oh duniya ina za ki da mu? Yau na ga rayuwa, tabbas inda ranka ka sha kallo.A can xaki sun yi jigum cike da jimami, haka ne ya sa Ainau ta yi zaton ko tunkiyar ce ta mutu, ta miqe ta nufi soron. Ganin akuyar ta yi da sauri ta koma xaki.Abbana me ya sami tunkiyar?Ba su iya ce mata komai ba sum-sum ta fice tsakar gida ta koma ta ci gaba da duba littafinta.*** *** ***Washegari kamar yadda ya saba qarfe shida na safiya suka xauki hanya, inda Ainau ke sanye da kayan makaranta. Iro ya sa ta a gaba sun yi tafiya mai nisa kafin su isa makarantar su Ainah sai da ya tabbatar da ta shiga aji, sannan ya koma ya nemi guri ya zauna a *** bishiyar dalbejiya yana jira a taso su. Tsawon awa guda yana faman karanta wasiqar jaki, a haka bacci ya yi awon gaba da shi. Lokacin da ya soma jin daxin baccin ne ya ji ana tava shi tamkar aa mafarki. A haankali ya ware idanunshi, mutumin da ya gani tsaye a gabansa ne ya sanya shi wartsakewa, a ruxe ya koma ya miqe cikin sauri ya tsaya a tagar ajin su Ainah. Hango ta ya yi zaune, ya sauke ajiyar zuciya ya nufi Isuhu don son jin abin da ke tafe da shi.Iro sarkin wayo da dabara, wallahi wayonka ba zai tseratar da ku ba, sai dai idan ni ne ban ga dama ba, kuma ina son ka sani kai na fito nema.Da sauri Iro ya dube shi, Ni kuma?Ya gyara tsayuwarsa cike da qeta.Zan yi maka gargaxi a kan abin da idanunka suka yi karambanin gane muku k...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters3
premium2
02

Book 2

Premium
Updated a year agoAvailable now
03

Book 1

Premium
Updated a year agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play