FreeArewaPen original
SULTAN MERAH
- 1views
- 43chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwa Manazarciya Marubuciya Ƴar kasuwa Chocolate addict 🍫 Bookworm📗 Introvert 😚
Sample · 1
*SULTAN MERA*Haske writers Association ©Fertymerh Xarah💞1Phoenix Wata sassanyar murya marar amo, wadda ke dauke da rashin kuxari ta yi sallama a dakin, ta amsar sallama tana kallon sa, sanye yake cikin shud'iyar shadda gexner wadda tayi matuqar fito da sirrin fuskar sa. (kallo d'aya na yi masa na gane shi din jinin Aiman mera ne saboda tsananin kama da suke da juna)SULTAN kenan mai shekara goma kacal a duniya. Duk wani fushi, bacin rai da ke cikin xuciyarshi sai yaji yana bacewa sanadiyar hada idanuwa da mahaifiyarshi Afiya. A hankali ya qarasa shiga dakin tare da yiwa kansa maxauni a d'aya daga cikin kujerun da suka yiwa qayataccen falon qawanya. 'me ya same ka haka? ta tambaya cike da kulawa irin ta d'a da mahaifiyar sa. Ya turo bakin sa tare da dauke kansa daga kallon ta, Mami wai meyasa sai nayi kwallo ne, na gayamasa bana son kwallo bata cikin tsarina a rayuwa, just look at me Mami dan Allah jikina yayi kama da na masu kwallo, meyasa Dad yaqi ya gane hakan?Taja numfashi kadan tana kallon sa, meyasa kai kuma baka jin magana ne, sau nawa kake so nayi ma mgn akan wannan, miye aciki dan ka faranta ran mahaifin ka, kayi masa abinda yake so?Ya qara tsuke qaramin bakin sa hade da yatsina fuskarsa, yana qoqarin tashi ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu. Look sultan dole ne xakayi abinda mahaifin ka ya umurce ka dashi matuqar baka son raina ya baci akan ka, mahaifinka bai kasance mai bijirewa umarni iyayen sa ba, tun yana yaron sa ya taso da son kasancewa d'an kwallo amma mai martaba ya hana sa yana so ya xama cikakken likita domin yana sha'awar ace yau jinin sa mai ceton al'umma ne, sai ya xamana bashi da aiki ko lokacin wani abu idan ba kallon ball ba sai karatun sa, ya baiwa kallon ball muhimmanci fiye da tunanin ka wanda alokacin ko mace bata gabansa, ya kasa cika burin sa na xama d'an kwallo amma ya cika burin iyayen sa wanda albarkar hakan ke tare dashi har kake ganin sa a matsayin da yake yanxu, meyasa kai baxaka cika masa burin na sa ba. Sultan ya dubi cikin dake jikin ta kafin ya motsa bakin sa da kyar yace, Mami ba gashi kina dauke da wani baby ba, ya bari idan kin haihu yaron ya cika masa burin sa amma ni ball baya cikin future plan d'ina, we have horses a gidan nan ni shine burina na xama d'an tseren doki. Allah ya kyauta sultan amma baa nan gidan ba, footballer xaka xama ko kana so ko baka so final decision din mu kenan, ta gefen karatun ka xaka iya xabar fannin da kake so ka xama in your future. Bai qara magana ba ya tashi xai fice ko me ya tuna ya juya yana kallonta kamar xai yi kuka. Mami ban daina wannan mafarkin ba, yau ma nayi and again naga taurarin biyu suna kusanto junan su. Ka cigaba da addua, nima Ina kan yi. Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya bac...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.