FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapte 1: page 1
WANI SONA ZEE YABOURFREE PAGE 01Kyakkyawar budurwa ce mai kimanin shekaru sha tara zaune kan stool na madaidacin madubin d'aki, shak'e yake da kayan ado da shafa kala kala, ta shafa wannan ta guga wancan, wanda hakan ke nuni yar' gayu ce mai son ado da tsafta, ta share kusan minti talatin zaune bakin madubin,"Jauhar shirin ne baki gama ba har yanzu, ko ganin gwamna zaki ai sai haka" Cewar Matashiya wacce ba zata gaza shekaru talatin da biyar ba, Ta d'an sunkuyar da kanta alamar jin kunya tana murmushi, Kumatun ta suka lotsa dimple d'inta dake k'ara k'awata fuskarta ya bayyana, Yaya deeja tace "Ko da yake wannan so da ake yiwa Jameel ai yafi ganin gwamna", Murmushin ta sake yi ba tare da ta kalli Yaya deeja ba, "Ni dai shawarar da nake baki ko da yaushe itace ki sassauta son da kike mishi, ban ce kar ki so shi ba, amma WANI SO idan yayi yawa ya kan zama cuta", Kanta ta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.