FreeArewaPen original
FURAR DANƘO....!
- 1views
- 155chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
........Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.